DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Matatar man Dangote dake Najeriya ta sanar da dawo da wasu daga cikin ma’aikatanta na injiniyoyin da ta ladabtar da su wajen tura su aiki a wasu ma’aikatu, sakamakon wani laifi da suka yi a baya.
Sanarwar da kamfanin dillancin labarai ya fitar ya ce dawo da waɗannan ma’aikata ya biyo bayan afuwar da akai musu bayan ɗaukar matakan ladabtarwa ta cikin gida.
Kotun ƙoli ta kori ƙarar PDP ɓangaren Tanimu Turaki
Jaridar The Cable ta wallafa cewaa ƙasar ta ɗauki matakin dawo da ma’aikata bakin aikin su, ya biyo bayan sanya hannu da kuma roƙo daga wasu manyan mutane da masu ruwa da tsaki a harkar mai da kuma injiniyoyin da abin ya shafa.
Jaridar ta ce Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin, na Daya daga ciki, ya ce za’a gayyaci injiniyoyin wata ganawa kafin su koma bakin aikin su a matatar dake unguwar Lekki a Lagos.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, ma’aikatan da aka dawo da su sun haɗa da waɗanda suka ki karbar sauyin wurin aikin da aka musu a baya.
Kamfanin Dangoten ya ce wannan wata sabuwar dama ce da aka bai wa ma’aikatan wajen ganin sun gyara halin su tare da zama masu da’a da kuma nuna kwarewa wajen mutunta dokokin aiki.
Yace wannan mataki na Daya daga cikin matakan kamfanin, ya Kara tabbatar da aniyar su ta tabbatar da ɗa’a da kuma bin ka’idodin aiki ba tare da yin zagon ƙasa ba.
Daga karshe, kamfanin ya ce duk wanda aka Kara kamashi da samu ya aikata wani laifi nan gaba daga cikin waɗannan injiniyoyi, za’a kore shi kai tsaye.
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewar sun fuskanci kalubale da dama daga cikin ma’aikatan matatar, ciki harda waɗanda suke haɗa baki da wasu daga waje domin yiwa kamfanin zagon ƙasa wajen lalata masa kayan aiki
