Gwamna Abba Ya Rungumi Akidar “Kano First” Bayan Fatali Da Tsarin Kwankwasiyya Da Ya yi; Abin Da Ya yi Siyasa ce ko Sabon Tsari?
Daga Abdullahi Yusuf, Mohammed Kabir Ya’u,Salisu Ibrahim, Abbas Ibrahim,Mustapha Muhammad,Kabiru Fulatan
A jihar Kano, muhawara na ci gaba da ƙara zafi kan matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na sauya sheƙa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP zuwa All Progressives Congress APC, tare da ƙaddamar da wata sabuwar manufa mai taken “Kano First”.
Matakin dai ya zo ne a wani lokaci da ake ci gaba da fuskantar sauye-sauye a siyasar Kano, musamman dangane da dangantakar da ke tsakanin gwamnan da tsohon jagoransa na siyasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ake danganta shi da tafiyar Kwankwasiyya.
Tun kafin wannan sauyi, an dade ana hasashen cewa akwai baraka tsakanin Gwamna Abba da jagoran Kwankwasiyya, duk da cewa ba a fito fili an tabbatar da hakan ba.
Wasu masu sharhi na ganin cewa sabanin ra’ayi kan yadda za a tafiyar da mulki da kuma batun ikon siyasa ne suka haifar da wannan rabuwar kai.
Kwankwasiyya, wadda aka san ta da tsari mai karfi da kuma biyayya ga jagoranci, na kallon wannan sauyi a matsayin barazana ga akidarta, wadda ta dade tana jan ragamar siyasa a Kano.
Amma Gwamnatin Kano ta bayyana cewa manufar “Kano First” wata cikakkiyar falsafar shugabanci ce da ke nufin: fifita muradun Kano sama da duk wani tasiri na siyasa, tare da farfaɗo da tattalin arzikin jihar, inganta ababen more rayuwa, da kuma ƙarfafa cibiyoyin gwamnati.
A cewar jami’an gwamnati, wannan manufa za ta taimaka wajen dawo da Kano a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, ta hanyar jawo jari da kuma bunƙasa kasuwanci.
Masana harkokin siyasa na cewa sauya jam’iyyar na iya sauya tasirin siyasa a Kano baki ɗaya. Wasu na ganin cewa shiga jam’iyyar APC zai bai wa gwamnan na Kano damar samun goyon bayan gwamnatin tarayya, wanda zai iya taimaka masa wajen aiwatar da manufofinsa.
Sai dai kuma akwai fargabar cewa wannan mataki na iya jawo rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya, musamman waɗanda suka taka rawa wajen tabbatar da nasarar gwamnan a zaɓen baya.
Magoya bayan Kwankwasiyya na ci gaba da nuna rashin jin daɗinsu, suna masu cewa wannan mataki ya saba da amincewar da suka yi wa gwamnan. Wasu daga cikinsu sun bayyana sauyin a matsayin “cin amanar siyasa”.
A gefe guda kuma, wasu magoya bayan gwamnan na goyon bayan matakin, suna cewa lokaci ya yi da za a fifita ci gaban Kano fiye da biyayya ga Shugaba ko kuma wani tsari na siyasa.da ake alakantawa da shugaban.
Masu sharhi da dama sun danganta ƙaddamar da “Kano First” da shirye-shiryen zaɓen 2027. A ra’ayinsu, wannan manufa na iya zama wata hanya ta jawo hankalin jama’a da kuma gina sabon tubalin siyasa.
Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya musanta wannan zargi, yana mai cewa manufar ba ta da alaƙa da neman tazarce, illa kawai an ƙaddamar da ita ne domin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban Kano.
Duk da kyawawan manufofin da aka bayyana, masana na cewa akwai ƙalubale da dama da ke gaban wannan manufa, ciki har da:
yadda za a samu goyon bayan dukkan ɓangarorin siyasa, aiwatar da manufofi cikin gaskiya da riƙon amana, da kuma magance matsalolin tattalin arziki da kuma tsaro.
Har ila yau, wasu na ganin abubuwan da suka faru a farkon mulkin gwamnan, ciki har da rushe-rushe da aka yi wa wasu gine-gine, na iya ci gaba da tasiri a kan yadda jama’a za su karɓi wannan sabuwar manufa.
