Shugaban Kwango Brazzaville, Denis Sassou Nguesso na kasancewa shugaba a nahiyar Afirka da ya fi dade wa kan karagar mulki bayan takwarorinsa na Kamaru, Paul Biya da kuma Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Eauatorial Guinea.
Shugaban ƙasar Congo-Brazzaville, Denis Sassou Nguesso, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga Maris, 2026, domin ƙara tsawaita mulkinsa da ya shafe sama da shekaru 40 yana yi.
Sassou Nguesso mai shekaru 82, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi gaban dubban magoya bayansa a yankin Ignie, a kudancin ƙasar, inda ya ce: “Zan tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa.”
Congo-Brazzaville, wadda ke da yawan jama’a kusan miliyan shida, ƙasa ce mai yalwar man fetur, amma rahotanni sun nuna cewa kashi huɗu cikin ɗari kacal na ƙasar ne ake noma, lamarin da ya sa take dogaro sosai da abincin da ake shigo da shi daga waje, abin da ke barazana ga tsaron abinci sakamakon tashin farashin kayayyaki a duniya.
Sassou Nguesso na ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi daɗewa kan karagar mulki, bayan Paul Biya na Kamaru da Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea. Jimillar mulkinsa ta kai shekaru 42, duk da hutun shekaru biyar da ya yi daga mulki.
Ya fara mulkin ƙasar ne daga 1979 zuwa 1992 a ƙarƙashin tsarin jam’iyya ɗaya, kafin ya sha kaye a zaɓen jam’iyyun da yawa na farko a hannun tsohon Firaminista Pascal Lissouba. Sai dai ya koma kan mulki a 1997 bayan ya kifar da Lissouba ta hanyar yaƙin basasa, kuma tun daga lokacin yake kan madafun iko.
Sassou Nguesso ya ci zaɓe a 2002 da 2009, sannan kuma a 2016 da 2021 ƙarƙashin sabon kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima. A shekarar 2015, ya amince da gyaran kundin tsarin mulki da ya cire iyakar wa’adin shugabanci da kuma sharadin shekaru ga masu neman takara.
