Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya Horon Kwanaki Biyu,Ga “Ƴan Jaridar Yanar Gizo A Dutse,Jihar Jigawa
Daga Amina Fagge
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirin ta na inganta aikin jaridar yanar gizo bisa Inganci, ɗa’a da ƙwarewa, inda ta bayyana kafafen yaɗa labaran a matsayin ginshiƙi wajen tafiyar da dimokuraɗiyyar Najeriya
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake buɗe taron horaswar na kwanaki biyu ga mambobin kafafen yada labarai na zamani (Kano Online Media Chapel) na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), yayin da Kwamishinan yace an shirya horon ne kacokan da goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano, don basu horo na musamman la’akari da tasirin su a cikin al’umma
Anyiwa Taron Take da“Ƙarfafa Aikin Jaridar Intanet ta Hanyar Aiki Bisa Ɗa’a da Hulɗar Yanar Gizo mai Dorewa don Cigaban Jama’a.”
Waiya ya ce wannan horo, shi ne irinsa na farko ga masu wallafa jaridun intanet a Jihar Kano, ya nuna yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kallon aikin jarida a matsayin muhimmin ɓangare na tafiyar da ayyukan dimokuraɗiyya.
Kwamishinan ya yi kira ga ‘yan jaridar masu wallafa labarai ta yanar gizo intanet da su riƙa bin ƙa’idojin ɗabi’a, ƙwarewa da gaskiya wajen tattarawa da yaɗa labarai, yana jaddada cewa dole ne a bambanta aikin jaridar intanet da ayyukan kafafen sada zumunta marasa tsari.
Ya ce: “’Yan jaridar yanar gizon ba ɗaya suke da masu amfani da kafafen sada zumunta ba. Aikin jarida na zamani dole ne ya kasance bisa doka da oda, ba wai tayar da hankali ko gaggawar fitar da labari ba tare da tantancewa ba.”
Waiya ya ƙara da cewa saurin bunƙasar dandalin intanet, tare da fitowar sabbin fasahohi kamar basirar (AI), ya sanya wajibi ‘yan jarida su ci gaba da sabunta ilimi da ƙwarewa domin su saje da bukatun ƙasa da ƙasa.
Shima a Nasa Bangaren Dayake jawabi Shugaban Kungiyar Mawallafa Jaridar Intanet Kwamaret Abubakar Dangambo ya godewa Gwamnatin Jihar Kano da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida bisa goyon bayan da suka bayar, inda ya bayyana taron a matsayin wani ginshiki wanda yazo daidai da zamani.
Ya yi kira ga mambobin kungiyar da su ci gaba da aiki bisa ƙa’idojin aikin jarida, tare da bin dokoki da tanade-tanaden zamantakewa da na shari’a na Jihar Kano.
Taron ya samu halartar ‘yan jaridu daga kafafen yaɗa labarai na intanet daban-daban da ke aiki a faɗin Jihar Kano.
A Ƙarshe dai taron yasamu halartar Manyan frofesoshi da dactoci daga Jami ar Bayero, kamar su Dr.Saminu Umar ,Prof.Nura Ibrahim,Dr.Saminu Shehu Ibrahim,dama wasu da Dama Wadanda Duka sun gabatar da Makala Akan Horon.
