Jam’iyyar ADC Ta Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Sabuwar Dokar Haraji Ta Kasa
Daga Abdullahi Yusuf
Jam’iyyar ADC ta soki Gwamnatin Tarayya a kan sabuwar Dokar Haraji Ta Kasa,ta na mai cewa dokar za ta kara jefa “Yan Nigeria cikin halin kuncin tattalin arziki da rashin walwala.
Wannan suka kuwa na kunshe ne a cikin sakon Barka Da Kirsimati na Jam’iyyar wanda Mataimakin Sakatarenta na tsare-tsare na kasa,Ali Tukur Gantsa,ya rattabawa hannu.
A cikin sanarwar dai,Ali Gantsa, tsohon sakataren Jami’yar PDP a jihar Jigawa Kuma sakataren tsare stare shiyar Arewa maso yamma, ya taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar Kirsimati,ya na mai yin Addu’a ga Allah da ya sanya “Yan Nigeria su shiga cikin sabuwar shekara cikin zaman lafiya da karuwar arziki.
Daga nan sai Jam’iyyar ta nuna damuwarta a kan halin rashin tsaro a cikin kasa, wanda ta ce ya takura wa “Yan Nigeria, kuma ya kawo kin yarda da Gwamnati saboda gazawarta wajen cika alkawuranta na kare lafiyarsu da dukiyarsu.
Ali Gantsa,wanda kuma tsohon Sakataren Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ne, kuma tsohon Sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar PDP, Shiyyar Arewa maso Yamma,ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tashi tsaye wajen maganta matsalar tsaro da ta addabi kasa baki daya.
Daga nan sai ya yi wa Gwamnati da mutanen Jihar Kano ta’aziyya a kan rashin “Yan Majalisar Dokokin Jihar guda biyu, wadanda su ka rasu a rana daya,ya na mai jimamin rashinsu,tare da cewa rasuwar ta su wani babban rashi ne ga Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Sannan kuma Jam’iyyar ta ADC ta yi ta’aziyya ga Gwamnatin Jihar Barno da iyalan wadanda su ka rasu a harin bam da “Yan Ta’adda su ka kai a wani Masallaci a Jihar,ya na mai kira da a kara daukar matakai wajen kare “Yan Kasa daga hare-haren “Yan Ta’adda.
Daga karshe Jam’iyyar ta ADC ta yi kira da a sami hadin kai da kaunar juna tsakanin “Yan Nigeria, da kuma shugabanci na gari a cikin kasa.
