Hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya (NSCDC) ta sanar da hukunta jami’anta 79 saboda laifuffuka daban-daban da suka haɗa da cin hanci, damfarar aikin yi, sata, sakaci, da karya ƙa’idojin aiki.
DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Daga cikin jami’ai 37 da aka sallame su daga aiki, yayin da wasu ke fuskantar shari’a da hukuncin ritaya ta dole.
Babban kwamandan NSCDC, dakta Ahmed Audi, ya ce cikin waɗanda aka sallama akwai jami’ai biyu na rundunar Mining Marshals da aka samu da laifin gudanar da aiki ba tare da izini ba, lamarin da ya haddasa mutuwar kwamandansu a Jihar Nasarawa.
Hakazalika hukumar ta kama mutum 18 da ake zargi da lalata bututun mai, satar kayan layin dogo, lalata kayayyakin wutar lantarki da kuma safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Babu Hidimar Ƙasa Ga Wanda NERD Ba Ta Tantance Ba – NYSC
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wanda aka tare a Enugu da makaman soja, alburusai da wasu kayayyakin da ake zargin na haɗa bama-bamai ne.
NSCDC ta ce za ta ci gaba da ɗaukar mataki kan duk wani jami’i ko farar hula da aka samu da laifi, tare da kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri domin kare muhimman kadarorin ƙasa.
PRNIGERIA
