Rundunar Sojin Nijeriya ta ce matar wani babban jami’in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da ɗanta mai shekara 11 sun miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin Kai a ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a ranar Asabar, ya ce bincike ya nuna cewa mijin matar, wanda shi ma babban kwamandan ISWAP ne, ya miƙa wuya tun ranar 25 ga Yuli.
Haɗin Gwiwar Gwamnati Da Ƙungiyoyin Fararen Hula Zai Haɓaka Ci Gaban Kano – Bilkisu Indabo
Sanarwar ta ce bayan ya miƙa wuya, shi ne ya umurci matarsa ta fito daga maɓoyarsu tare da ɗansu domin su miƙa wuya ga sojoji.
Rundunar ta bayyana cewa an riga an tantance matar da ɗanta, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai da gudanar da bincike a kansu bisa doka.
A wani samame na daban kuma, sojoji sun kama mutum shida da ake zargin suna taimaka wa mayaƙan ISWAP wajen gudanar da harkokinsu a wasu sassan Jihar Borno.
Bincike ya nuna cewa ana zargin mutanen da taimaka wa ƙungiyar wajen samun kuɗaɗen shiga ta hanyar kasuwancin dabbobi a kasuwannin Gubio, Damasak da Ajuwango.
Haka kuma, rundunar ta ce mayaƙan ISWAP sun tsere bayan wani samame da dakarun suka kai yankin Turoh bisa bayanan sirri da suka samu.
Bayan binciken yankin, sojojin sun ƙwato babura guda biyu da kuma tarin miyagun ƙwayoyi da mayaƙan suka bari a wurin.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da hare-hare bisa sahihan bayanan sirri domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabashin ƙasar.
