Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ce sama da malamai 200 sun bar aikin jami’ar saboda rashin kyawun yanayin aiki da kuma gazawar aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma da kungiyar a shekarar 2025.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Shugaban ASUU na reshen KASU, Dr Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Kaduna.
Ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar na kara jefa malaman jami’ar cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka bar aikin.
Saboda haka, kungiyar ta bai wa mahukuntan jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu da su fara aiwatar da yarjejeniyar tare da tabbatar da an yi aiki da tanade-tanadenta a jami’ar.
Almajirai 4 Sun Rasa Ransu Bayan Cin Kifi A Kano
- ASUU ta kuma gargadi mahukuntan jami’ar cewa, idan ba a dauki matakan da suka dace cikin wa’adin da ta kayyade ba, za ta shiga yajin aikin gama-gari da ta ce zai kasance mai tsauri kuma na sai baba-ta-gani.
