Jami’an tsaro a Jihar Bauchi sun dakile wani yunƙurin sace ɗalibai a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati (Government Girls’ College) da ke jihar, bayan wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi ƙoƙarin shiga harabar makarantar.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe huɗu na asubahin ranar Lahadi 15 ga watan Maris, lokacin da wasu mutane suka yi yunƙurin tsallaka katangar makarantar ta wani ɓangare da ke kusa da gidajen ma’aikata.
Hatsarin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ya jikkata mutane da dama
Jaridar TheCable, wadda ta ruwaito rahoton daga majiyar tsaro Zagazola Makama, ta ce masu gadin makarantar sun fara hango motsin mutanen tare da sanar da jami’an tsaro da ke sintiri a yankin.
Bayan samun wannan bayani, jami’an tsaron sun garzaya wurin cikin gaggawa, abin da ya sa waɗanda ake zargin sun tsere daga wurin kafin su aiwatar da shirin da ake zargin sun zo yi.
Rahoton ya ce yunƙurin harin ya janyo ɗan firgici a cikin makarantar, inda wasu ɗalibai suka fara ihu sakamakon tsoron abin da ke faruwa.
Sai dai hukumomin tsaro sun ce babu wata ɗaliba da aka sace ko kuma aka samu rahoton rauni sakamakon lamarin.
Jami’an tsaro sun kuma bayyana cewa an ƙara tsaurara sintiri da matakan tsaro a kewayen makarantar domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari.
Hukumomin sun ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano mutanen da suka yi yunƙurin harin tare da cafke su.
