Mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan wayar da kai da haɗa kan al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta ƙaddamar da wani shiri na musamman da nufin fito da nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu tare da ƙarfafa hulɗa da jama’a a faɗin jihar.
An tsara gudanar da taron ne a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a ɗakin karatu na Murtala Muhammad Library, inda za a gabatar da cikakken bayani mai tushe kan ayyukan da gwamnatin ta aiwatar tun bayan hawanta mulki.
INEC Ta Yi Gargadi Kan Yin Rijistar Katin Zaɓe Sau Biyu
Indabo ta bayyana cewa shirin zai haskaka manyan ci gaban da aka samu, musamman a fannonin gine-ginen more rayuwa da gyaran birane, tare da sauran nasarori a ɓangarorin tattalin arziki, zamantakewa da siyasa.
Ta jaddada cewa wannan ƙoƙari na daga cikin dabarun gwamnati na tabbatar da cewa jama’a na samun sahihin bayani kan ayyukan gwamnati, tare da ƙarfafa su shiga cikin harkokin tafiyar da mulki ta hanyar gaskiya da buɗaɗɗen bayani.
Shirin, a cewarta, zai taimaka wajen ƙara amincewar jama’a da gwamnati, inganta ɗaukar alhaki, da kuma samar da damar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma wajen ci gaban jihar.
An gayyaci masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-daban da suka haɗa da ƙungiyoyin farar hula, ƙwararru, ƙungiyoyin matasa da ‘yan siyasa domin halartar taron, a wani yunƙuri na tabbatar da tattaunawa mai faɗi da kuma haɗin kai wajen cimma muradun ci gaban Kano.
Masu sa ido sun bayyana cewa wannan shiri na daidai da ƙoƙarin da gwamnatin Yusuf ke yi na ƙarfafa manufofinta na gyara, tare da jan hankalin jama’a ta hanyar nuna ayyuka a zahiri da kuma ci gaba da hulɗa da al’umma.
