Author: Idris Musa

Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharazu, ya buƙaci Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) da ya ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) bayan kammala aikin rajista. Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) na Ɗan Malikin Kano, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, wanda ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa Fadar Karaye domin neman goyon bayan masarautar wajen ƙarfafa wayar da kan jama’a kan muhimmancin rajistar katin zaɓe. Ya yabawa kwamitin bisa ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa al’umma…

Read More