Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja na duba yiwuwar haramta zirga-zirgar baburan haya (Okada) da Adaidaita Sahu (Keke Napep) a wasu sassan tsakiyar birnin Abuja saboda matsalolin tsaro.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Wike ya ce matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin tsaro na FCT, bayan rahotannin sirri sun nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da babura wajen gudanar da ayyukansu.
Ya ce an umarci hukumomin tsaro su tantance wuraren da za a hana zirga-zirgar babura da Adaidaita Sahu, tare da amincewa da samar da kayan aiki domin ƙarfafa ayyukan tsaro. Sai dai ya bayyana cewa ba zai yiwu a hana su aiki a daukacin Abuja ba saboda bukatun sufuri.
Yan Bindiga Sun Sace Tawagar Daukar Amarya a Katsina
Har ila yau, Wike ya koka kan yadda mabarata ke ci gaba da komawa Abuja duk da kokarin mayar da su jihohin da suka fito, yana mai cewa kasancewar Abuja na tsakiyar jihohi da dama na kara janyo wannan kalubale.
