Daga Zainab Kamal Ibrahim
Akalla mata 500 ne suka hallara a unguwar Gwammaja da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano domin gudanar da saukar karatun Alƙur’ani mai girma tare da addu’o’in neman zaman lafiya da kawo ƙarshen ayyukan daba da kashe-kashen matasa da suka addabi yankin.
Jami’an EFCC Sun Kama Shugaban Hukumar Makamashi Kan Badaƙalar Naira Biliyan 500
Shugabar ƙungiyar da ta shirya taron, Hajiya Halima Musa Abdullahi, ta bayyana cewa makasudin gudanar da taron shi ne neman taimakon Allah kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashen da ake yi wa matasa marasa laifi.
Ta ce lamarin ya jefa iyalai da dama cikin alhini da fargaba, duba da yadda bata-gari ke shiga unguwanni suna aikata ta’asa ba tare da tausayi ba.
”Mun shirya wannan taro ne domin neman zaman lafiya da kuma roƙon Allah Ya kawo ƙarshen wannan matsala da ta addabi al’umma, musamman matasa,” in ji ta.
Hajiya Halima ta kuma yi kira ga iyaye maza da mata da su ƙara kula da tarbiyyar ‘ya’yansu domin gujewa fadawa cikin ayyukan daba da sauran miyagun halaye.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar “Dala Ina Mafita” ya bayyana cewa sun fara ɗaukar wasu matakan tsaro a yankin domin rage yawaitar ayyukan bata-gari da tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce sakacin wasu iyaye wajen kula da tarbiyyar yara na daga cikin dalilan da ke haifar da matsalar rashin ɗa’a a tsakanin matasa.
“Allah Ya ɗora wa iyaye amanar ‘ya’yansu, kuma wajibi ne su kula da su domin gina al’umma ta gari,” in ji shi.
Ita ma Hajiya Aisha Dalhatu, wadda tana daga cikin iyayen da rikicin ya shafa, ta yi Allah wadai da kashe-kashen da suka jawo mata rasa ɗanta.
Ta buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan gaggawa domin hukunta masu hannu a kashe-kashen tare da samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar daba a Kano.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana matuƙar damuwarsu kan yadda wasu matasa suka rasa rayukansu tare da ƙone wasu a cikin gidajensu, lamarin da suka ce ya ƙara jefa al’umma cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali.
