Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake gargadin jama’a da su guji yin rijistar katin zaɓe fiye da sau ɗaya, tana mai cewa hakan laifi ne da ke da hukunci mai tsauri a ƙarƙashin dokar zaɓe.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Hajiya Nahila Bello Dandago, ce ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa a gidan rediyon Kano a ranar Asabar. Ta ce duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifi na iya fuskantar ɗaurin kurkuku ko tara, ko ma duka biyun.
Gwamnatin Kano Ta Tura Dalibai 550 Domin Taimakawa Wajen Faɗaɗa Rajistar Katin Zaɓe A Fadin Jihar
Ta ƙara da cewa baya ga hukuncin doka, hukumar na kuma ɗaukar matakan ladabtarwa a tsarin zaɓe, ciki har da goge duk wani rajista da aka maimaita, abin da ka iya hana mutum damar kaɗa ƙuri’a.
Hajiya Dandago ta kuma jaddada ƙudirin INEC na ƙara yawan masu rajista a faɗin ƙasa, inda ta ce an ƙaddamar da wani shiri na musamman domin faɗaɗa cibiyoyin rajista, wanda aka fi sani da “mega registration”.
A cewarta, an samar da damar yin rajista ta yanar gizo domin sauƙaƙa wa jama’a, sai dai ta nanata cewa dole ne a je wurin rajista domin ɗaukar bayanan biometric kafin a kammala aikin.
Hakazalika, ta ce hukumar na fitar da jerin sunayen masu rajista lokaci zuwa lokaci domin bai wa jama’a damar duba bayanansu tare da yin gyara idan akwai kuskure.
A nasa bangaren, wani mamba a kwamitin CVR Taskforce, Abbas Ibrahim, ya ce suna ci gaba da wayar da kan jama’a domin ƙarfafa shigar su cikin rajistar masu zaɓe.
Ya bayyana cewa an tura ɗalibai 550 daga manyan makarantu tara a jihar domin taimaka wa jama’a wajen yin rajista ta yanar gizo, a wani yunkuri na tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta ya samu damar shiga cikin tsarin zaɓe.
