Gwamnatin Jihar Kano ta tura dalibai 550 daga cibiyoyin ilimi tara domin taimakawa wajen faɗaɗa rajistar rajistar masu zaɓe CVR, a wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya a faɗin jihar.
Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a filin wasanni na Kofar Mata, inda ake gudanar da babban aikin rajistar masu zaɓe.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abbas Ibrahim, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, ya fitar a madadin Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano.
A cewar Waiya, an horas da daliban domin su taimaka wajen yin rajista ta yanar gizo (online pre-registration), domin rage cunkoso da kuma hanzarta aikin rajistar kai tsaye, musamman ga ɗalibai da sauran al’umma da ke fuskantar matsalar isa cibiyoyin rajista.
Ya ƙara da cewa daga cikin daliban, 100 sun fito ne daga Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, yayin da sauran cibiyoyi takwas suka samar da dalibai 50 kowacce.
Waiya, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, ya jaddada cewa rajistar masu zaɓe muhimmin hakki ne na ɗan ƙasa, wanda ke taka rawa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci.
Ya ce: “Wannan wata dama ce ga matasa su bayar da gudunmawa wajen gina dimokuraɗiyya. Jajircewarku da gaskiyarku za su taimaka wajen tabbatar da cewa an samu cikakken wakilci a tsarin shugabanci.”
Ya kuma buƙaci daliban da su gudanar da aikinsu da gaskiya da riƙon amana, tare da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa, yana mai gargadin su guji duk wani abu da zai kawo tarnaki ga sahihancin aikin.
A wani ɓangare kuma, ya bayyana cewa za a karrama daliban da suka fi ƙwazo da nuna nagarta wajen gudanar da aikinsu, domin ƙarfafa gasa mai kyau da kuma ɗaukar nauyi.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta taka muhimmiyar rawa wajen horas da daliban kan fannoni na fasaha da ɗabi’a da suka shafi rajistar masu zaɓe.
Haka kuma, shugabannin cibiyoyin ilimin da abin ya shafa sun halarci wajen ƙaddamar da shirin domin sanya ido, lamarin da ke nuna cikakken goyon bayan hukumomi ga shirin da kuma muhimmancin rawar da matasa ke takawa.
Wasu daga cikin daliban da aka zaɓa sun bayyana shirinsu na yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar shirin, tare da jaddada aniyarsu ta taimakawa wajen ƙara yawan masu rajista a jihar.
