Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP nan take.
Kwankwaso, wanda ya kasance jagoran jam’iyyar na kasa kuma dan takararta a zaben shugaban kasa na 2023, ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan nazari kan yanayin siyasar kasar, domin samun wata sabuwar hanya da za ta ba shi damar kawo sauyi mai ma’ana.
WAEC: Ɗalibai Sama da 10,000 Sun Rubuta Jarabawa, Kashi 32% Sun Samu Credits Biyar
Ya gode wa shugabannin jam’iyyar, ciki har da shugaban jam’iyyar, Ajuji Ahmed, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake jam’iyyar.
Haka kuma ya yaba wa dukkan mambobi da magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya bisa jajircewarsu, yana mai cewa za su ci gaba da hada kai domin ganin an gina kyakkyawar makoma ga Najeriya.
