Kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC guda dubu ɗaya da ɗari biyar (1,500) da aka yi wa rajista sun amince da marawa shirin Renewed Hope Network (TRN) na Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin wata kafa ta musamman da aka ƙirƙira domin wayar da kan jama’a domin tabbatar da sake zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a shekarar 2027.
Wata sanarwa da Mataimakin Darakta Janar na gamayyar kungiyoyin, Dakta AK Peters, ya sanya wa hannu a Abuja, ta bayyana cewa bayan wani muhimmin taro, TRN ƙarƙashin jagorancin gogaggen mai wayar da kan jama’a na APC kuma tsohon Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban APC na Ƙasa kan harkokin ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin goyon baya, Kwamared Okpokwu Ogenyi, tare da Farfesa Tunji John Asaolu, wanda fitaccen jami’in diflomasiyya ne, ya nuna cikakken kwarin gwiwa kan yadda TRN ke samun karɓuwa a faɗin Najeriya baki daya.
Kano: Gwamnati ta musanta rahoton cewa Sarki Sanusi zai jagoranci hawan Sallah
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari ne mai daukar nauyin ayyukan Renewed Hope Network (TRN), a matsayin wata kafa ta wayar da kan jama’a a daga tushe, domin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A cikin shirye-shiryen farko na dabarun lashe zabe, TRN ta fara tattara sunayen wakilan jam’iyya a dukkan rumfunan zaɓe a faɗin Najeriya, domin gina inganta hulɗa da jama’a.
Peters ya ce TRN na samun karɓuwa a wurin ‘yan Najeriya a kowane yanki na kasar, ya na mai cewa wannan yunkuri abin yabawa ne matuka.
A cewarsa, TRN ta tanadi tsare-tsare da dabaru da nufin tabbatar da gagarumar nasara ga Shugaba Tinubu a shekarar 2027.
Ya ce, “TRN ta kuduri aniyar gina tsari mai inganci tun daga tushe domin bawa Mai Girma Shugaban Ƙasa dukkan wani goyan baya da ya ke bukata domin sake lashe zabe a 2027.
“A jam’iyyar APC muna da fiye da ƙungiyoyin goyon baya 3,500 da aka yi wa rajista, daga cikinsu 1,500 sun amince da haɗin gwiwa da TRN. Muna da yaƙinin cewa shauran 2,000 za su shiga wannan tafiya daga yanzu zuwa lokacin bikin Easter.”
Shugaban Majalisar ya ce ta hanyar la’akari da nagartaccen jagoranci da Sanata Abdulaziz Yari ke bayarwa, Renewed Hope Network ita ce babbar kafa da ke aikin tabbatar da goyon bayan jama’a daga tushe a faɗin Najeiya baki daya.
Ya ƙara da cewa idan kungiar ta co gaba da samun goyan baya daga Sanata Yari, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen neman goyon bayan ‘yan Najeriya domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
