Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci hawan Sallah mai zuwa a jihar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, sanarwar ta ce rahoton da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta ba shi da tushe.
Jami’an tsaro Sun Dakile Yunƙurin Sace Ɗalibai A Kwalejin ’Yan Mata A Bauchi
Ta bayyana cewa har yanzu ba a yanke wani hukunci a hukumance dangane da batun jagorancin hawan Sallah ba.
Gwamnatin ta ƙara da cewa batun masarautar Kano na gaban kotu, don haka ya dace a bar ɓangaren shari’a ya gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.
Haka kuma, ta ce tana tsaka-tsaki a takaddamar da ke tattare da masarautar, inda ta nisanta kanta daga dukkan ɓangarorin har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe.
Gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita, tare da dogaro da sahihan bayanai daga majiyoyi na hukuma.
Har ila yau, ta bukaci kafofin yaɗa labarai da masu amfani da shafukan sada zumunta da su riƙa tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗa su, domin kauce wa haifar da ruɗani ko tashin hankali, musamman yayin da ake shirin bukukuwan Sallah.
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada ƙudirin ta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.
