Kotun Shari’ar Musulunci ta Upper Sharia Court Shahuci da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Abdu Abdullahi Wayyah, ta yanke hukunci kan wani matashi da aka samu da laifin dukan wani mutum har ya samu karaya.
Kotun ta samu matashin mai suna Hassan Abba, mazaunin unguwar Durumin Iya – Lokon Maraba, da laifin kai wa wani matashi mai suna Ibrahim Haruna hari, lamarin da ya haddasa masa karaya a mukamuki.
Bayanai da suka fito daga kotun sun nuna cewa wanda aka samu da laifin na daga cikin matasan da ake kira masu sukuwa da doki a bayan Gidan Sarkin Kano, duk da cewa hukumomi sun haramta irin wannan abu saboda matsalolin tsaro da tashin hankali da ke faruwa a wasu lokuta.
Bayan nazarin shaidu da bayanan da aka gabatar a gaban kotu, Alƙali Abdu Abdullahi Wayyah ya yanke wa Hassan Abba hukunci kamar haka:
Daure shi watanni uku a gidan gyaran hali ko kuma ya biya tara ta naira 30,000.
Yin aikin tsaftace harabar masallacin Gidan Sarkin Kano na tsawon wata guda a matsayin hukuncin non-custodial sentence.
Biyan kuɗin magani naira 293,350 ga wanda ya ji rauni, wato Ibrahim Haruna.
Bugu da bulala 12 a matsayin wani ɓangare na hukuncin da kotun ta zartar.
Kotun ta bayyana cewa hukuncin na da nufin zama darasi ga matasan da ke shiga ayyukan sukuwa da doki da kuma duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali a cikin al’umma.
