Kwamitin Kula Da Tashoshin Mota Ya Mika Gurbatattun Kwayoyi Na N1.5bn Ga Hukumar DMCSA Ta Jihar Kano
Daga Abdullahi Yusuf
Kwamitin Kula Da Tashoshin Mota na Jihar Kano ya mika gurbatattun kwayoyi da ya kwace na kudi kimanin N1.5b ga Hukumar Samar Da Magunguna Ta Jihar Kano,wato DMCSA,domin adana su, kafin a batar da su.
Wannan labari ya na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Jami’in Hudda da Jama’a na Hukumar ta DMCS,Farouk Isa Musa,ya bayar.
Yayin da ya ke mika kwayoyin, Shugaban Kwamitin,Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya ce, kwayoyin wadanda su ka hada da na bogi da wadanda su ka daina aiki,ya ce an kama su ne a Kasuwar Magani ta Dangwauro.
Manjo Usman ya ba da tabbacin cewa Kwamitin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa a na yin aiki da ka’idojin kula da kiwon lafiya a Jihar Kano,kuma zai rika aiki kafada-da-kafada da shugabannin Kasuwar Magani ta Dangwauro domin cin ma wannan buri.
“Mu na aiki tukuru domin kiyaye lafiyar mutane,kuma duk wanda mu ka samu ya na kokarin kawo mana cikas za mu dauki mataki a kansa.Kuma mu na kira ga masu sai da Magunguna da sauran kwayoyi da su rika lura da dokokin sai da su,kuma su rika bai wa mutane shawarar sayen magani daga sahihan diloli,” in ji shi.
Lokacin da ya ke karbar kwayoyin, Shugaban Hukumar ta DMCSA,Pharm. Gali Sule, ya jaddada kudirin Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da kula da lafiyar mutanen Jihar.
“A madadin Hukumar DMCSA ina mai karbar wadannan gurbatattun kwayoyi na bogi,da wadanda su ka daina aiki,a cikin tsananin damuwa,” in ji Pharm. Gali Sule.
Ya ce, “wadannan kwayoyi su na kawo cikas wajen kula da lafiyar mutane, har su kan haddasa rasa rayuka, saboda haka, wannan Hukuma za ta ci gaba da ganowa da hukunta masu baza haramtattun Magunguna a kasuwanninmu.”
Daga nan sai Shugaban Hukumar ta DMCS ya yaba wa Kwamitin saboda jajircewarsa a kan aikinsa,wanda ya ce ya kare lafiyar mutane da dama.
Pharm. Sule ya kuma yi kira ga masu shigo da Magunguna daga kasashen waje,da masu rarrabasu da sayar da su,da Malaman Asibiti,da su rika lura da ka’idojin sarrafa Magunguna.
Sannan ya yi kira ga Jama’a da su rika sayen magani daga sahihan diloli,su kuma kai rahoton duk wasu Magungunan bogi da su ka gani.
Kwayoyin da a ka mika wa Hukumar ta DMCS sun hada da 199 cartons na Benzhexol Hydrochloride BP 5mg tablets, 5 cartons na Cinbul tablets, Levofloxacin 500mg, 3 cartons na Cikatetem 60 ml, 6 cartons of Betaclox, da kuma 80 packets na Augementin 1g.
