SIYASAR KANO
Lallai kam, yanzu Kano, birninta da kauyukanta, tudu da kwarinta,ta dauki Harami da Gangami na hada-hadar Siyasa,gabanin Babban Zaben shekarar 2027,wato badi ke nan.
Tun farkon watan Janairu a ka fara ganin alamun dumamar yanayin Siyasar Kano,har zuwa ranar 23 ga shi wannan wata,wadda a cikinta ne Maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf,ya fita daga Jam’iyyar NNPP, kuma bayan kwanaki uku da yin hakan,wato ranar 26 ga watan Janairu,ya koma Jam’iyyarsa ta ainahi, wato APC.
Wannan mataki da Maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf,ya dauka,ya kawo karshen duk wasu jita-jita da hasahe da a ka dade a na yi a fagen Siyasar Kano na komawar Gwamnan Jam’iyyar APC,ko akasin hakan.
Yanzu dai ta faru ta kare.Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma Jam’iyyarsa ta ainahi,wato APC,kuma ya fadi dalilinsa na yin hakan,wato domin ci gaban Jihar Kano,bunkasarta da zaman lafiyarta.
Muna rokon Allah Subhanahu Wata’ala da ya sanya albarka a cikin wannan Sabuwar Tafiya ta Maigirma Gwamna,ya kuma ba shi Iko da Kwarin Gwiwar ci gaba da aiwatar da ayyukan alheri da ya bijiro da su cikin fiye da shekaru biyu da su ka wuce.
Muna kuma rokon Allah Subhanahu Wata’ala da ya dauwamar da zaman lafiya, karuwar arziki da walwala a Jihar Kano,da ma sauran sassan Nigeria baki daya.
Naku,
Abdallahi Yusuf.
