Shekaru 78 da suka gabata, a shekarar 1948, ƙasar Costa Rica ta ɗauki wani mataki da har yanzu ƙasashe da dama ke kallonsa a matsayin abin mamaki, inda ta rusa rundunar sojinta gaba ɗaya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasar, José Figueres Ferrer.
Matakin bai samo asali daga yalwar zaman lafiya ko wadata ba, sai dai daga darasin siyasa mai ɗaci da ƙasar ta koya bayan wata gajeriyar amma mummunar arangama ta yaƙin basasa. A lokacin, jama’a da dama sun gaji da yadda rundunonin soji ke zama kayan aikin juyin mulki da tsoratarwa a ƙasashen Latin Amurka.
Shugabannin Costa Rica sun yi imanin cewa yawaitar ƙarfin soja na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya da kwanciyar hankali. Saboda haka suka yanke shawarar rusa rundunar soji domin kare tsarin farar hula da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Maimakon karkatar da dukiya wajen sayen makamai da faɗaɗa rundunonin yaƙi, gwamnatin ƙasar ta mayar da hankali wajen bunƙasa ilimi, lafiya, gine-ginen more rayuwa da kuma ƙarfafa hukumomin farar hula.
Hukumomin ’yan sanda ne suka zama ginshiƙin tsaron cikin gida, yayin da gwamnati ta fara gina al’umma bisa tunanin haɗin kai, tattaunawa da mutunta doka maimakon mulkin tsoro da ƙarfin bindiga.
A hankali, matakin ya sauya fasalin ƙasar gaba ɗaya.
Kuɗaɗen da da ana warewa harkokin soja sun koma makarantu, asibitoci, yawon buɗe ido da shirye-shiryen ci gaban jama’a. Daga bisani, Costa Rica ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen Latin Amurka mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali duk da rikice-rikicen siyasa da suka addabi yankin.
Sai dai rusa rundunar soja bai hana ƙasar fuskantar ƙalubale ba.
Costa Rica ta sha fama da takaddama da maƙwabciyarta Nicaragua, tare da barazanar safarar miyagun ƙwayoyi da ayyukan masu laifi. Duk da haka, ƙasar ta guji komawa tsarin mulkin soja ko sake gina rundunar yaƙi.
Maimakon haka, ta ƙarfafa ayyukan tattara bayanan sirri, tsaron cikin gida, diflomasiyya da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, musamman United States.
Masu sharhi na ganin cewa ba kowace ƙasa ce za ta iya kwaikwayon tsarin Costa Rica ba, la’akari da yanayin siyasarta da ƙanƙantar yawan jama’arta. Sai dai tarihin ƙasar ya ci gaba da tayar da muhawara kan illar dogaro da ƙarfin soja fiye da kima.
A sassa da dama na duniya, rundunonin sojin da aka kafa domin kare ƙasa sun rikide zuwa cibiyoyin iko da ke iya barazana ga dimokuraɗiyya ta hanyar juyin mulki, murƙushe ’yancin jama’a da karkatar da kuɗaɗen al’umma wajen sayen makamai.
Amma Costa Rica ta zaɓi wata hanya dabam.
Bayan sama da shekaru saba’in, ƙasar na ci gaba da zama abin koyi cewa girman ƙasa ba ya ta’allaka ga yawan makamai ko ƙarfin soja, sai dai ga ƙarfafan hukumomi, wayewar kai da kuma fifita tattaunawa sama da amfani da ƙarfi.
