Shugaban riko na Federal College of Agricultural Produce Technology (FCAPT) da ke Kano, Dakta Salisu Salisu, ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa kafa Kwamitin Kar-ta-Kwana kan Sabunta Rajistar Masu Zaɓe (CVR), yana mai cewa matakin ya taimaka wajen kusantar da aikin rajistar katin zaɓe ga ɗalibai da sauran al’umma.
Dakta Salisu ya bayyana hakan ne yayin gudanar da aikin rajistar katin zaɓe a harabar kwalejin, inda ya ce yadda aka kai cibiyoyin rajistar zuwa makarantu da sauran wuraren taruwar jama’a ya sauƙaƙa wa ɗalibai da ma’aikata damar yin sabuwar rajista ko sabunta bayanansu cikin sauƙi.
Ya ce aikin na gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, abin da ya nuna jajircewar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa ya samu damar mallakar katin zaɓe domin cika haƙƙinsa na dimokuraɗiyya.
Shugaban kwalejin ya ce hangen nesa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna wajen kafa Kwamitin Kar-ta-Kwana kan CVR ya taimaka matuƙa wajen wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa su su fito domin yin rajista kafin ƙarewar wa’adin da INEC ta gindaya.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da Hukumar INEC, bisa haɗin gwiwar da suke yi wajen tabbatar da nasarar aikin sabunta rajistar masu zaɓe a sassan ƙasar.
A ƙarshe, Dakta Salisu ya yi kira ga ɗalibai, ma’aikata da sauran al’umma da su yi amfani da damar da ake da ita wajen yin rajistar katin zaɓe ko sabunta bayanansu kafin wa’adin da Hukumar INEC ta ƙayyade ya ƙare.
