DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama Darakta-Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya (ECN), Mustapha Abdullahi, bisa zargin almundahanar kuɗi.
Kishi Ya Rikide Zuwa Tashin Hankali Yayin Da Mace Ta Kona Kishiyarta Da ’Ya’yanta A Kano
Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta ce an kama shi ne a Abuja, kuma a halin yanzu yana hannun hukumar domin ci gaba da bincike.
Majiyar ta ce ana zargin cewa kuɗaɗen da ake binciken sun kai kusan Naira biliyan 500.
Har yanzu EFCC ba ta fitar da cikakken bayani a hukumance ba, kuma ƙoƙarin jin ta bakin kakakinta bai yi nasara ba.
An naɗa Mustapha Abdullahi a matsayin shugaban hukumar makamashi ta ƙasa a watan Oktoba 2023.
An naɗa Mustapha Abdullahi Shugaban ECN bayan ya shafe fiye fa shekaru 10 yana aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur NUPRC.
