Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sunayen bankuna 33 da ya amince cewa jarinsu ya kai su ci gaba da gudanar da hada-hada a cikin ƙasar, a wani yunƙuri na kare dukiyoyin abokan hulɗarsu.
Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a jiya Laraba, ya ce shirin wanda aka soma tun watan Maris na shekarar 2024, an kammala shi a yanzu bayan shafe watanni 24 ana yinsa, domin ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi tsakanin bankuna da abokan hulɗarsu a Najeriya.
Babban bankin ya ce bankunan 33 da aka amince dasu sun samar da jari na Naira tiriliyan 4 da biliyan 650 ƙarƙashin sabon shirin da ya ƙaddamar.
CBN ya ce shirin ya samu karɓuwa sosai a wajen masu zuba jari na cikin gida da kuma waje, inda kashi fiye da 72 na jarin ya zo daga cikin ƙasar, yayin da kashi 27 ya zo daga abokan hulɗa na ƙasashen waje.
Manyan bankuna da suke hada-hada ta ƙasa da ƙasa, sun cika sharaɗin da aka gindaya musu na samun jarin da ya haura Naira biliyan 500, cikinsu akwai bankin GT, da FCMB, da Fidelity, da Zenith, da Access, da Firstbank, da kuma UBA.
To sai dai CBN ya ce zai yi ƙarin bayani game da bankin Polaris da Keystone da kuma Union da a halin yanzu suke kasancewa ƙarƙashin kulawarsa, wanda tunda fari gwamna Olayemi Cardoso ya ce ba lallai su kasance cikin sabon tsarin ba, saboda matsaloli da suke fuskanta.
