Ana zargin wani mutum da yanka matarsa, Fatima Muhammad, da kuma ɗansu Masaud Nazir da wuka a unguwar Samaigu da ke Jihar Kano.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Rahotanni sun ce mutumin ya caka wa matarsa wuka a gefen cikinta, yayin da ɗansu ya samu raunuka a hannunsa da kuma kansa.
Wata maƙwabciyar iyalan ta tabbatar wa wakilinmu cewa lamarin ya faru, sai dai ta ce ba ta da cikakken bayani kan yadda abin ya faru ko kuma abin da ya haddasa rikicin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin faruwar lamarin ba, kuma babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan abin da ya jawo harin.
A wani ɗan gajeren bidiyo da aka aike wa wakilinmu, an ga Masaud Nazir ɗauke da raunuka a hannunsa da kuma kansa.
An garzaya da Fatima Muhammad da ɗanta zuwa Asibitin Murtala Mohammed da ke Kano, inda suke ci gaba da karɓar kulawar likitoci.
