Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PRP, Donald Duke, ya bayyana cewa iƙirarin cewa Najeriya ce ƙasa mafi arziki a Afirka “ƙarya ne”.
Tsohon gwamnan Jihar Cross River ya ce a maimakon haka, Najeriya na daga cikin ƙasashe mafi talauci a nahiyar, kuma bai kamata a kira ta tattalin arziki mafi girma a Afirka bisa la’akari da jimillar mau’aunin tattalin arziki na GDP kawai ba.
A wata hira da wasu ’yan jarida a Legas, Duke ya ce Najeriya ƙasa ce mai ƙarancin arziki idan aka yi la’akari da kudin shiga ga kowane ɗan ƙasa (per capita income).
Ya ce har ma wasu ƙasashen da Najeriya ke ganin sun fi ta ƙanƙanta suna da mafi yawan kudin shiga ga kowane mutum, yana mai cewa ƙasar tana “rayuwa cikin ƙarya”.
“Abin kunya ne cewa ƙasar da a da ake kallonta a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe mafi arziki a Afirka har yanzu tana ganin ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka. Wannan ba gaskiya ba ne.
“Muna rayuwa cikin ƙarya. Yana da daɗin ji a ce Najeriya ce mafi girman tattalin arziki a Afirka. A’a. Najeriya na daga cikin ƙasashe mafi talauci idan aka yi la’akari da kudin shiga ga kowane mutum. Wannan shi ne abin da ya kamata a auna, ba wai ci gaban GDP kaɗai ba.
“Ko da duk abin da muke samarwa a Najeriya shi ne kulikuli, kamar yadda aka ba mu shawara mu yi, har yanzu za mu kasance da babban GDP. Amma idan aka zo ga kowane mutum, yaya ƙarfin tattalin arzikinsa yake? Yana da rauni sosai.
“Yawancin ƙasashen da muke yi wa dariya suna da kudin shiga ga kowane mutum da ya fi namu yawa.
“Don haka, komai ya koma kan samar da inganci. Hankalin da ba ya aiki fili ne na shaidan. Hakan gaskiya ne jiya, gaskiya ne yau, kuma zai kasance gaskiya gobe,” in ji Duke.
Da yake magana kan matsalar tsaro, Duke ya ce ba ya son amfani da kalmar “’yan ta’addan Musulunci”, saboda bai yarda cewa Musulunci ne ke samar da ’yan ta’addan ba.
Ya ce matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta, musamman a yankin arewacin ƙasar, sun ƙara muni ne sakamakon rugujewar Libya, lamarin da ya haifar da kwararar makamai ta kan iyakokin Najeriya.
Saboda haka, ya ce Najeriya na buƙatar matakai na gajeren lokaci, matsakaicin lokaci da dogon lokaci domin magance matsalar rashin tsaron da ke hana ci gaban ƙasar.
“Yanzu dole ne ku magance matsalolin tsaro kamar yadda suke a yau , garkuwa da mutane, ’yan bindiga, ta’addanci da sauran makamantansu.
“Amma bayan haka, waɗannan abubuwa sakamakon wasu matsaloli ne. Sakamakon tattalin arziki mai rauni ne da kuma gazawar kula da iyakokinmu yadda ya kamata.
“Bayan rugujewar Libya, makamai da yawa sun fara shigowa kudu. Muna kiransu ’yan ta’addan Musulunci. Ba na son wannan kalma saboda ban yi imanin cewa Musulunci ne ke sanya su ba.
“Musuluncin da na sani ya bambanta. Suna amfani da wannan suna ne kawai wajen bayyana su. A ganina, su mutane ne masu aikata barna. Ana iya ganin hakan idan suka shiga cikin al’umma, inda suke karɓar haraji da yin wasu abubuwa. Duk abin da suke yi yana da nasaba da tarawa ko gina tushen arziki domin kansu.”
A batun samar da ayyukan yi da amfani da fasaha, Duke ya ce a matsakaici da dogon lokaci, ya kamata gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali wajen sa ’yan ƙasa su kasance masu samar da kayayyaki da ayyuka yadda ya kamata.
Ya ce muddin mutane ba sa yin ayyukan da ke samar da arziki, za su nemi hanyoyin rayuwa da kansu.
Ya shawarci gwamnati ta mai da hankali kan samar da kayayyaki a cikin gida domin inganta yawan aiki da kuma amfani da fasahar zamani wajen kare iyakokin ƙasar.
Da yake magana kan farfaɗo da tattalin arzikin Arewacin Najeriya, ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai tabbatar da cewa an tsara ayyukan hakar ma’adinai a yankin yadda ya kamata.
A cewarsa, tsarin ya kamata ya bai wa al’ummomin yankin damar shiga cikin harkar ma’adinai, tare da tabbatar da cewa ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi sun zama masu ruwa da tsaki a fannin.
“Gaggawar neman samar da mai ba ta nufin arziki kai tsaye ba. Dole ne a samu adadi mai yawa da zai dace da kasuwanci da sauran abubuwa. Wani lokaci ina ganin an fi ɗaukaka batun fiye da yadda yake. Man da ake zargin yana cikin tafkin Chadi ba ya nan cikin adadin da zai dace da kasuwanci. Ina ganin ainihin arzikin Arewa, bayan noma, yana cikin ma’adinan da ke cikinsa.
“Dole ne a samu tsari mai kyau na hakar ma’adinai. A yau, ana yin hakan ne ta hanyar ƙananan masu hakar ma’adinai, kuma al’umma, musamman waɗanda ke zaune a kan iyakoki, da ƙasa baki ɗaya ba sa samun isasshen amfani daga waɗannan albarkatu.
“Misali, ku dubi zinaren Zamfara. Wataƙila ban sani ba, yana iya kasancewa da zinare mai yawa kamar na Ghana baki ɗaya. Ghana a wani lokaci ana kiranta da Gold Coast, don haka hakan ya nuna irin yawan zinaren da zai iya kasancewa a Zamfara. Amma hakar ma’adinai ya kuma jawo matsalar ’yan bindiga saboda Najeriya ba ta da isasshen tsaro a wurare da dama.
“Saboda haka, zan mayar da kowace jiha wata cibiyar tattalin arziki. Ina ganin hakan zai ƙarfafa jihohi da gwamnatocinsu su mayar da hankali kan ma’adinan da suke da su.
“Idan ni ne ke jagoranci, tare da jihohi, za mu gudanar da bincike. Na san an riga an yi wasu daga cikin irin wannan binciken. Za mu tantance abin da ake da shi a kowace jiha, sannan mu ƙara zurfafa bincike domin gano adadin ma’adinan da aka tabbatar da samuwarsu.
“Misali, idan ana neman columbite ko wani ma’adini kuma an san yana samuwa a wani wuri, za mu ƙara bincike domin gano adadin columbite, lithium ko duk wani ma’adini da muke son haɓakawa da aka tabbatar da samuwarsa.
“Da zarar an kai matakin nan, hakan zai sa masu zuba jari su fi sha’awar shigowa. Ya kamata gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya su gudanar da hakan a matsayin haɗin gwiwa, saboda za a raba kudaden shiga daga waɗannan albarkatu tsakanin matakan gwamnati biyu.
“Amma babu wanda zai zuba jari idan babu tsaro. Mun ga abin da ya faru a Kudu, musamman yankin Neja Delta, lokacin da tsaro ya lalace, wanda kuma ya samo asali ne daga ƙara tsanantar talauci a yankunan.
“Masu zuba jari a can , kamfanonin mai da na ƙasa da ƙasa sun fice, kuma yanzu sun fi son hako mai daga cikin teku mai zurfi, wanda ake ganin ya fi samun tsaro,” in ji shi.
