- Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta ƙwato na’urorin hasken rana (solar) guda 160 da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 59.2, waɗanda ake zargin wani magidanci mai shekaru 43 ya sace tare da ɓoye su a wani kango da ke unguwar Haye, cikin yankin Sharaɗa.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Kakakin rundunar ya bayyana cewa nasarar ta samu ne a wani samame da jami’an ’yan sanda suka gudanar bayan samun sahihan labarai na sirri, inda aka gano tare da ƙwato kayayyakin da ake zargin an sace.
GECCI Ta Bukaci Gwamnati Ta Inganta Manufofin Kiwo Domin Tallafa Wa Makiyaya
Haka kuma, rundunar ta kama wasu magidanta uku da ake zargi da hannu a fashin famfon man fetur na wani gidan mai da ke Ƙaramar Hukumar Gaya.
An kiyasta darajar kayayyakin da aka kwato daga hannunsu da yakai kimanin Naira miliyan 10.2.
A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun bayyana sun sayi kayan ne daga wani mutum ɗan asalin Jihar Kaduna. Sai dai mutumin ya tsere kafin jami’an tsaro su samu nasarar cafke shi, kuma ana ci gaba da farautarsa.
Rundunar ta tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba, tare da alƙawarin kamo duk wani da ke da hannu a aikata laifin domin gurfanar da shi a gaban kotu.
