An gano gawar wani ɗalibi na Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK) da ya ɓace kwanaki kaɗan da suka gabata a cikin wani tafkin ruwa mara gudana da ke ƙauyen Sabon Garin Yero, kusa da garin Kashere a Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Marigayin, mai suna Enoch Sunday Maisamari, mai shekaru 28, ɗalibi ne a matakin shekara ta biyu a Sashen Microbiology na Tsangayar Kimiyya ta jami’ar.
Mutane 68 Sun Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Jirgin Enugu Air Ya Yi Saukar Gaggawa A Benin
Rahotanni sun bayyana cewa an ga Maisamari a karo na ƙarshe ne ranar Lahadi yayin wani bikin kammala karatu da ɗaliban shekarar ƙarshe na jami’ar suka shirya. Tun daga lokacin aka rasa inda yake, lamarin da ya jefa iyalansa da abokan karatunsa cikin damuwa.
Wata majiya ta shaida cewa jami’an ’yan sanda ne suka gano gawarsa a cikin tafkin ruwan, sannan suka sanar da hukumomin jami’ar. Daga bisani, ɗaya daga cikin abokan karatunsa ya tabbatar da cewa gawar tasa ce.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu rahoton gano gawar da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Laraba.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa an garzaya da gawar zuwa Asibitin Gwamnati da ke Kashere, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
Ya ƙara da cewa binciken farko bai nuna wata alamar tashin hankali a jikin mamacin ba, sai dai rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin mutuwarsa.
Hukumomin jami’ar da jami’an tsaro sun buƙaci al’umma da su guji yaɗa jita-jita, tare da jiran sakamakon binciken da ake ci gaba da yi kan lamarin.
