Aƙalla mutane 68 da ke cikin wani jirgin saman kamfanin Enugu Air sun tsallake rijiya da baya bayan da jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Benin da ke Jihar Edo a ranar Alhamis.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Rahotanni sun ce jirgin mai lambar 5N-ENR na kan hanyarsa daga Enugu zuwa Benin, kafin ya ci gaba da tafiya zuwa Legas, lokacin da lamarin ya faru.
Wata majiya daga filin jirgin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa bayan jirgin ya sauka, ya kauce daga hanyar saukar jirage tare da shiga wani yanki mai ciyayi da ke gefen titin jirgin.
Darajar Fasfon Nijeriya Ta Sauka Zuwa Matsayi na 90 a Duniya — Rahoton Henley
Nan take jami’an Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) suka isa wurin domin gudanar da aikin ceto, inda suka fitar da dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin cikin aminci.
Babu rahoton mutuwa ko samun munanan raunuka a hatsarin, yayin da hukumomin da abin ya shafa suka fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.
Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jami’an ceto suka gudanar da aikin fitar da fasinjojin daga jirgin cikin gaggawa.
