Fasfon Nijeriya ya sake yin ƙasa a sabon jerin darajar fasfunan ƙasashen duniya na Henley Passport Index, inda ya sauka zuwa matsayi na 90 a duniya, yayin da ya kasance na 45 a nahiyar Afirka.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Rahoton watan Yulin 2026, wanda kamfanin Henley & Partners ya fitar, ya nuna cewa masu riƙe da fasfon Nijeriya na iya shiga ƙasashe 44 ba tare da neman biza kafin tafiya ba.
Sabon matsayin ya nuna cewa Nijeriya ta yi ƙasa da matsayi ɗaya idan aka kwatanta da rahoton Afrilun 2026, inda ta kasance a matsayi na 89. Sai dai duk da saukar, adadin ƙasashen da masu fasfon Nijeriya ke iya shiga ba tare da biza ba bai sauya ba.
Ana Zargin Likitan El-Rufai Da Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
Kamfanin Henley & Partners ya bayyana cewa ana tantance ƙarfin fasfon kowace ƙasa ne bisa yawan ƙasashen da masu riƙe da shi za su iya shiga ba tare da samun biza kafin tafiya ba, ta hanyar amfani da bayanan Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA).
Rahoton ya kuma zo ne a daidai lokacin da kamfanin ke bikin cika shekaru 20 da ƙaddamar da wannan tsarin tantance darajar fasfunan ƙasashen duniya.
