Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta gayyaci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, domin yi masa tambayoyi kan rawar da ake zargin ya taka a batun wata hukuma da ta janyo ce-ce-ku-ce bayan an bayyana cewa ba ta da sahalewar gwamnati
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Lauyan Gbajabiamila, Jiti Ogunye, ya tabbatar da cewa ya bayyana a hedikwatar ICPC a ranar Litinin, inda jami’an hukumar suka masa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi PFIPC. Sai dai ya ce ya amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa tare da ba da haɗin kai ga masu bincike.
Binciken na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kafa PFIPC da kuma mutanen da ke da hannu a lamarin, bayan da aka bayyana cewa hukumar ba ta da wata doka ko amincewar gwamnati da ta halatta kafuwarta.
Darakta Ya Kai Hukumar JSC Ta Kano Kotu Kan Ritayar Dole, Ya Nemi Diyyar Naira Miliyan 100
Har yanzu ICPC ba ta fitar da cikakken sakamakon binciken ba, amma ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma ɗaukar matakin da ya dace idan an samu wata hujjar karya doka.
