A ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, 2026, an gudanar da bikin aure biyu a Masallacin Anas Bin Malik da ke unguwar Sheka Achilafiya, inda iyalai da abokai suka hallara domin shaida wannan muhimmin biki.
Bikin ya hada auren Aliyu Abdullahi Idris, wanda aka fi sani da “Butter”, da Hauwa’u U. Abdullahi Alhassan. Haka kuma a wannan rana aka daura auren Khadija Abdullahi Idris da Usman Ismail.
Mutane sama da 50 sun rasu a kuskuren harin sojin sama a kasuwa
Mahaifin ango da amarya, Abdullahi Idris, ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarar gudanar da bikin lafiya, tare da yaba wa dukkan wadanda suka halarta domin taya su murna.
Limamin masallacin, Malam Ibrahim, shi ne ya jagoranci daurin auren, inda ya yi nasiha ga ma’auratan kan muhimmancin hakuri, fahimtar juna da kuma mutunta juna a zaman aure.
Bikin ya gudana cikin yanayi na farin ciki, tare da addu’o’i da fatan alheri ga sabbin ma’auratan.
