Cibiyar Terra Academy for the Arts (TAFTA), tare da haɗin gwiwar Mastercard, ta horar da matasa 28,000 a Jihar Kano domin ƙarfafa tattalin arziki da rage rashin aikin yi.
Manajan shirin na TAFTA a Kano, Abubakar Balarabe, ya bayyana a wani taro da aka gudanar a Kano cewa shirin na haɗa koyon sana’o’i da damar samun aikin yi ko kafa kasuwanci.
Ya ce an horar da matasa a fannoni daban-daban kamar animation, rubutun shiri (scriptwriting), fasaha, kasuwanci, ƙirar sauti da hasken dandalin wasan kwaikwayo, inda shirin ya shafi Kano, Lagos da Ogun.
Balarabe ya bayyana cewa shirin, wanda yanzu ya shiga shekara ta huɗu a Kano, yana bai wa mata matasa fifiko, domin rage rashin aikin yi a tsakanin su da kuma fa’idar da ke tattare da ƙarfafa su ta fuskar tattalin arziki.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka samu horo sun nuna farin ciki da shirin. Wata ɗaliba da ta horar a ƙirar sauti ta ce shirin ya buɗe mata sabuwar kasuwa.
Haka kuma, Fatima Saleh, wadda ta samu horo a rubutun shiri, ta bayyana cewa shirin ya ƙara mata ƙwarewa wajen inganta kasuwancinta, har ma ya ba ta damar sake komawa koyon animation domin tallata kayayyakin ta ga duniya.
Shirin TAFTA na daga cikin matakan da ake ɗauka domin bai wa matasa damar samun ilimi da ƙwarewa, musamman a fannin kere-kere da fasaha, domin rage rashin aikin yi a Najeriya.
