Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama matasa sama da 250 kan yin askin banza ko kuma kitse gashinsu.
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Mujahid Aminudden ne ya bayyana haka a bayanin da ya fitar game da ayyukan rundunar a bikin karamar Sallah.
Ya ce daga cikin matasan akwai matuka Adaidaita Sahu da ke daukan mata a gefen baburansu.
Gabanin bikin Sallar dai, hukumar ta fitar da sanarwar gargadi musamman ga matasa, kan kiyaye ayyukan da suka saba da tanadin addini da al’adun mutanen Kano.
