Kano Ta Yi Cikar Kwari
“Ta Dabo Sha Baki;Ta Dabo Tumbin Giwa;Kamisulu Alfun; Mai Mata Mai Mota, Mai Tumaki Mai Jakai; Yaro Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka;Kano Garin Zaman Lafiya Da Walwala.”
Wadannan duk kirarin Kano ne.Allah Ya albarkanci wannan Gari da ke Kudu da Sahara.
Yanzu ne fa Kano ta ke shan Baki,har ma a na ganin cewa ta sha su har iya wuya, saboda irin mutanen da ke yin tururuwa zuwa cikinta daga ko ina cikin kasar nan, musamman ma Jihohin Arewa, na kusa da na nesa.
Daga cikin mutanen da ke shigowa cikin Kano kullu yauwin, akwai masu zuwa saye da sayarwa, Almajirai da kuma “Yan Gudun Hijira.Wadansu daga cikin wadannan rukunonin mutane in sun shigo sun yi harkokinsu su kan koma inda su ka fito,amma wadansunsu su na zama ne na dindindin.
Wadanda su ka fi zaman dirshan a Birnin Kano da kewanta su ne Almajirai da kuma wadanda su ka yiwo Gudun Hijira daga Jihohinsu ko don yanayin tsaro ko kuma yin kasuwawanci, ganin cewa Kano ce ta fi kowacce Jiha zaman lafiya da walwala a Arewacin Nigeria.
Wadannan abubuwa da na zayyana sun sanya Birnin Kano da kewanta sun yi “Cikar Kwari” da mutane,motocin hawa da baburan Dan Sahu, kusan ko ina ka duba, babu masakar tsinke.
Daga cikin matsalolin da wannan cunkoso ya jawo kuwa, akwai dumamar yananyi,tarin shara, aikata manyan laifuka kamarsu sace-sace da kuma karya dokokin hanya.
Sai dai kuma, a na ganin cewa wannan yanayi ya kara bunkasa kasuwanci da ilimi, musamman ma na Addinin Musulunci a Kano,ga kuma karin yawan mutane wanda shi ma wani babban abu ne da a ke la’akari da shi wajen rabon arzikin kasa, sannan ga yawan mutane masu jefa kuri’ar zabe,da sauransu.
Gwamnatin Jihar Kano,karkashin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf,ta tunkari wannan Kalubalen,inda ta dauki matakai dabam-dabam domin saita abubuwa.
Daga cikin wadannan matakai akwai gina sabbin hanyoyi,fadadawa da gyara wadansu a cikin Birnin Kano da kewanta da hedikwatocin kananan hukumomi,domin rage cunkoson abubuwan hawa,tare da kara yawan motoci da ma’aikatan kwashe shara.
Sannan kuma Gwamnatin ta dauki matakan inganta tsaro ciki har da kaddamar da Hukumar nan ta samar da tsaro a cikin garuruwa da unguwanni,wato Kano State Neighborhood Watch Corps,tare da inganta Hukumar Hisbah,da sauran ayyuka na tabbatar da tsaro a cikin wannan hamshakiyar Jiha tamu.
A bangaren kula da dokokin hanya kuma, Gwamnatin ta Jihar Kano ta inganta Hukumar Kula Da Dokokin Hanya,wato KAROTA,inda yanzu ma’aikatanta su ke kokari sosai wajen saita zirga-zirgar abubuwan hawa a fadin Jihar.
Masha Allah.Mu na rokon Allah Subhanahu Wata’ala da ya kara wa Kano albarka,zaman lafiya da daukaka.
Wassalam.
Naku,
Abdullahi Yusuf.
