Jam’iyyar Labour Party ta bayyana cewa za ta gudanar da Zaben fitar Gwani na shugaban ƙasa na cikin gida ranar 23 ga Mayu, 2026, a matsayin shiri na tunkarar babban zaɓen 2027.
A lokaci guda, jam’iyyar ta dakatar da membobi 25 saboda zargin aikata abubuwa marasa kyau da suka saba wa ka’idojin jam’iyya.
Hukuncin ya fito ne daga taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar Talata, inda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ido.
Jam’iyyar ta ce za a miƙa jerin sunayen mambobi ga INEC ranar 15 ga Afrilu, 2026, yayin da Zaben fitar Gwani na gwamna da na ‘yan majalisa zai gudana ranar 15 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, jam’iyya ta fitar da jadawalin zaɓen cikin gida:
Ward Congress – 26 ga Maris
Zaɓen kananan hukumomi – 28 ga Maris
Zaɓen jihohi – 31 ga Maris
Babban taron jam’iyya (National Convention) – 11 ga Afrilu
A wani mataki na ladabtarwa, jam’iyyar ta dakatar da membobi 25 da ake zargin aikata abubuwa marasa kyau, ciki har da shiga ofishin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba. Wannan ya biyo bayan shawarar Kwamitin Sulhu, Sasanta Rikici da Ladabtarwa na jam’iyya.
Jam’iyya ta amince da ƙarin rajistar mambobi ta hanyar haɗa rajistar zamani da ta gargajiya, musamman a yankunan karkara, domin ƙarfafa dimokuradiyya da gaskiya a gudanarwar jam’iyya.
NEC ta nuna cikakken goyon baya ga shugabancin wucin gadi na Nenadi Usman, wanda Kotun Ƙoli ta tabbatar kwanan nan. Haka kuma, an amince da ayyukan Kwamitin Ayyuka na Ƙasa, Hukumar Aminci ta Jam’iyya, shugabannin Labour, da Alex Otti.
Jam’iyyar ta yi kira ga membobi su yi amfani da hanyoyin ciki wajen bayyana korafe-korafensu, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya kafin babban zaɓen 2027.
