A Jihar Kano, an ƙaddamar da wani shiri na kwanaki shida na rajistar Katin zaɓe, a wani yunƙuri na ƙara yawan masu katin zaɓe da kuma ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya.
Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Katin Zaɓe na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin a ranar Laraba a cibiyar wasanni da ke Kofar Mata.
A cewarsa, an tanadi rumfunan rajista guda 20 domin sauƙaƙa wa jama’a yin rajista cikin gaggawa da kuma rage cunkoso.
Waiya ya bayyana gamsuwarsa kan yadda jama’a suka fito domin yin rajistar, yana mai cewa hakan na nuna fahimtar al’umma kan muhimmancin zaɓe a tsarin mulkin dimokuraɗiyya.
Ya jaddada cewa rajistar zaɓe wajibi ne ga duk ɗan ƙasa da ya cancanta, domin ita ce hanya ɗaya tilo da za a iya zaɓar shugabanni ta hanyar kuri’a.
Waiya, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa shirye-shiryen da ke ƙarfafa dimokuraɗiyya a Kano.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano, Ambasada Abdu A. Zango, ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na ci gaba da sa ido kan yadda ake gudanar da rajistar, tare da tabbatar da bin ƙa’idoji.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta tabbatar da an gudanar da rajistar cikin gaskiya da adalci a faɗin jihar.
An tsara gudanar da shirin daga ranar 1 zuwa 6 ga watan Afrilu, 2026, daga ƙarfe 9 na safe zuwa 3 na rana a kowace rana.
Wannnan Sanarwar ta fito ne daga bakin Abbas Ibrahim, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, a madadin Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, a ranar 2 ga Afrilu, 2026.
