Wani rahotan hukumar da ke ƙididdige yawan jama’a na duniya ya sanya Kano a matsayi ta 9 cikin biranen da suka fi yawan jama’a a duniya.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Birnin ya shiga sawun birane da suka haɗa da Shanghai da Beijing da Shenzhen da Chengdu dake ƙasar China, sai kuma Delhi da Mumbai a ƙasar India da kuma Kinshasa a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Karachi a ƙasar Pakistan.
Gwamna Abba Kabir Ya Amince Da Karin Albashi Ga Ma’aikatan Jami’o’in Kano Guda Biyu
Waɗannan alƙaluma na Kano ana hasashen cewar na iya kaiwa miliyan 20 nan da shekara ta 2030, wanda ka iya samar mata da ci gaba idan an yi tanadi na musamman domin samarwa matasa sana’oin da za su dogara da kansu, ko kuma su zama mata matsala sakamakon rashin ayyukan yi.
