Shugaban Kasa Bola Ahmed Tunubu ya umurci Hukumar EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ta samu na dakatar da asusun gwamnatin jihar Osun.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tunubu ya ce ko da yake bai saba tsoma baki cikin ayyukan hukumomin yaki da cin hanci ba, ya damu da lokacin da aka bijiro da matakin ba, kasancewar jihar Osun na gab da gudanar da zaben gwamna.
Muna Da Ikon Dakatar Da Asusun Gwamnatin Jiha Har Na Tsawon Sa’o’i 72 Kafin Umarnin Kotu. EFCC
Shugaban ya ce bai san da matakin EFCC tun da farko ba, amma ya yi gargadin cewa bai kamata a dauki wani mataki da zai iya haifar da zargin cewa gwamnatin tarayya na kokarin yin tasiri kan zaben ba.
Saboda haka, ya ce ya umurci EFCC da ta janye umarnin kotun tare da dakatar da duk wani mataki da ta dauka kan gwamnatin jihar Osun domin kare mutuncin tsarin dimokuradiyya.
