Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta ce matakin da ta dauka na dakatar da asusun Gwamnatin Jihar Osun ya yi daidai da tanadin doka.
Daga Zainab Kamal Ibrahim
Daraktan hulda da Jama’a na hukumar, Wilson Uwujaren,ya bayyana cewa an dauki matakin ne bayan gano wasu mu’amala da ya tada zargi a asusun cikin makon da ya gabata, kuma ba sai an samu umarnin kotu ba kafin yin hakan.
WAEC Ta Rike Sakamakon Jarrabawar Dalibai 167,486
Ya ce dakatarwar ta shafi asusu guda daya kacal ne, ba wai an daskarar da dukkan asusun Gwamnatin Jihar Osun ba ne,kamar yadda wasu ke ikirari.
Uwujaren ya kara da cewa an gano ana tura makudan kudade daga asusun zuwa wasu kamfanoni da dama, lamarin da ya sa EFCC ta dauki mataki domin kare kudaden gwamnati da hana yiwuwar karkatar da su.
