DAGA ZAINAB KAMAL IBRAHIM
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, ya bayyana damuwarsa kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa, yana mai gargadin cewa hakan na iya yin illa ga tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya.
A ranar Litinin ne kotun da Mai Shari’a Peter Lifu ke jagoranta ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyun ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party da Zenith Labour Party (ZLP), bayan ta yanke hukuncin cewa jam’iyyun sun gaza cika wasu sharuddan kundin tsarin mulki da suka wajaba domin ci gaba da kasancewa cikin rijistar jam’iyyun siyasa.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba, Secondus ya ce wannan hukunci na iya rage damar shiga harkokin siyasa tare da raunana gasa ta dimokuraɗiyya idan aka bari ya tabbata.
Yayin da yake zargin gwamnati da yunƙurin raunana jam’iyyun adawa.
Secondus ya ce, Suna tsoron zaɓe ne abin da suke nema shi ne naɗa shugabanci kai tsaye ba tare da cikakkiyar gasa ba.
Ya kuma jaddada cewa tanadin kundin tsarin mulki game da soke rajistar jam’iyyu ya kamata a aiwatar da shi ne bayan kammala zaɓe, ba a tsakiyar tsarin zaɓe ba.
A cewarsa, soke rajistar jam’iyyun a wannan lokaci na iya tauye haƙƙin masu kaɗa ƙuri’a, haifar da rashin tabbas a harkokin siyasa, tare da takaita sararin dimokuraɗiyya, musamman a lokacin da wasu jam’iyyun ke fuskantar rikice-rikice.
Secondus ya bayyana matakin a matsayin barazana ga gasa mai inganci a tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ce Amincewa da ware wasu ɓangarorin siyasa ta hanyar rushe7 jam’iyyu a tsakiyar tsarin zaɓe wani abu ne da zai iya raunana dimokuraɗiyya.
Wannan mataki na haifar da gibi tare da rage kuzarin gasa da ake buƙata domin bunƙasar tsarin dimokuraɗiyya.
Tsohon shugaban na PDP ya ƙara da cewa ƙananan jam’iyyu da sabbin jam’iyyun siyasa suna da muhimmiyar rawa wajen faɗaɗa damar shiga siyasa da kuma tabbatar da wakilcin ra’ayoyi mabambanta a tsarin dimokuraɗiyya.
A cewarsa, dimokuraɗiyya mai ƙarfi tana buƙatar ba wa sababbin ra’ayoyi da ƙungiyoyi damar shiga fafatawar siyasa cikin sauƙi.
Sai dai kuma, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya har sai an kammala sauraron ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyun da abin ya shafa suka shigar.
