A Kano, mai bai wa gwamna shawara kan wayar da kai da haɗa kan al’umma, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka da suka shafi ilimi da lafiya, tare da ƙoƙarin ƙarfafa hulɗa da jama’a.
Ta ce daga cikin nasarorin da aka samu akwai gyaran makarantu a sassa daban-daban na jihar, da kuma ɗaukar nauyin karatun ɗalibai zuwa ƙasashen waje domin inganta harkar ilimi.
Haka kuma, ta bayyana cewa gwamnatin ta fara ɗaukar nauyin kula da lafiyar mata masu juna biyu a dukkan ƙananan hukumomin jihar, a wani mataki na inganta kiwon lafiya da rage mace-mace.
A cewar Indabo, ana shirin gudanar da wani taro domin wayar da kan jama’a da kuma bayyana waɗannan ayyuka, ciki har da matakin rage kuɗin makarantu da kashi 50 cikin 100.
Ta ƙara da cewa irin waɗannan matakai na nuna ƙoƙarin gwamnati wajen inganta rayuwar al’umma, tana mai cewa ba kasafai ake samun irin wannan tsari ba.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya ce gwamnatin na aiwatar da ayyuka da dama da suka shafi jin daɗin al’umma, kuma za a ci gaba da ƙara yawan ayyukan domin bunƙasa ci gaban jihar
Shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa gwamnatin na gudanar da ayyuka sama da 900 a fadin jihar.
Masu lura da al’amura sun ce waɗannan matakai na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na ƙarfafa ci gaba da kuma jawo hankalin jama’a wajen fahimtar ayyukan da ake aiwatarwa.
