A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA, ke fuskantar matsaloli wajen samun magunguna, duk da kasancewarsu cikin tsarin.
Shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA tsari ne na taimakekeniya domin tallafawa masu rauni, musamman mata da tsofaffi, domin samun kulawa ta musamman.
Bankin CBN Ya Fitar Da Sunayen Bankuna 33 Da Suka Cika Ƙa’idar Ƙara Jarinsu
Rahotanni sun nuna cewa, matsalar gudanar da shirin ta fi shafar mata da tsofaffi marasa lafiya.
Wakilanmu sun lura da cewa, matsalar ta fi k’amari a asibitin K’wararru na Asibitin Murtala Muhammad.
Asibitin na daya daga cikin manyan asibitocin da ke karɓar dimbin marasa lafiya daga ciki da wajen jihar.
Malama Hafsat, mai kimanin shekara 41 wadda ke fama da cutar asma, na daya daga cikin wadanda abin ya shafa. Ta koka da cewa duk lokacin da ta je Asibitin domin a duba lafiyarta, takan yi tafiya mai tsawo domin karɓar magunguna daga wani wuri dabam da bangaren da ake duba lafiyarta.
A cewarta, sau da dama tana tsallaka titi mai cunkoso tare da kananan yaranta, lamarin da ke jefa ta cikin hadari da kuma kara tsananta mata rashin lafiyarta.
“Wani lokaci ma wannan wahalar na iya tayar min da ciwon asma,” in ji ta.
Hafsat ta ce daga bisani ta hakura da tsarin, inda ta koma sayen magunguna daga kantuna masu zaman kansu, duk da karin kudin da hakan ke jawo mata.
Sai dai bincike ya nuna cewa ba ita kadai ba ce ke fuskantar irin wannan matsala. Wasu masu anfani da shirin, musamman masu karamin karfi, sun daina anfani da shi sakamakon irin wadannan kalubale.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa, duk da akwai wasu kantunan magunguna a cikin harabar bangaren jinya, ba sa cikin tsarin hukuma, abin da ke kara haifar da tambayoyi kan yadda aka tsara tsarin samar da magunguna.
Masu lura da al’amuran lafiya na cewa, wannan gibi na iya zama sakamakon matsalolin gudanarwa ko rashin daidaito tsakanin sassan aiki.
Haka kuma, batun ya janyo muhawara kan ko tsarin na cika ka’idojin da suka tanadi samar da ingantaccen kulawar lafiya ga ‘yan kasa.
An ruwaito cewa an tuntubi hukumomin da abin ya shafa domin jin karin bayani, amma har yanzu ba a samu amsa a hukumance ba.
Yayin da jama’a ke kara dogaro da irin wadannan tsare-tsaren lafiya, ana kira ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalar.
Masu sharhi na ganin cewa hada wuraren bada jinya da na karɓar magunguna wuri guda, tare da saukaka hanyoyin karɓar magani ga marasa lafiya, na daga cikin matakan da za su taimaka wajen rage wahalar da ake fuskanta.
