Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF ta kwace kofin zakarun nahiyar Afirka na 2025 daga ƙasar Senegal, tare da bai wa Morocco nasarar zama zakarun gasar.
Sanarwar da CAF ta fitar ta ce kwamitin sauraron ƙorafi na hukumar ya yanke hukuncin cewa tawagar Senegal ta karya dokokin gasar, bayan da wasu daga cikin ’yan wasanta suka fice daga filin wasa a yayin wasan ƙarshe domin nuna rashin amincewa da hukuncin alƙali.
Hukumar ta ƙara da cewa an ayyana Senegal da laifin watsi da wasa, wanda ya sa aka sauya sakamakon wasan daga 1-0 da Senegal ta samu zuwa 3-0 a hukumance domin Morocco.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa wasan ƙarshe na gasar ya gudana ne cikin yanayi mai cike da cece-kuce, musamman a ƙarshen lokaci inda aka bai wa Morocco bugun fenariti bayan duba VAR.
Hukuncin ya janyo fushin ’yan wasan Senegal, inda wasu suka dakatar da wasa na wani lokaci, lamarin da ya haifar da tsaiko na kusan mintuna 20.
A yayin rikicin, wasu daga cikin magoya bayan Senegal sun yi yunƙurin kutsawa cikin fili, tare da jefa wasu kayayyaki a cikin Filin, kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin.
A wasan dai, ɗan wasan Morocco Brahim Diaz ya kasa cin fenaritin, bayan mai tsaron ragar Senegal Edouard Mendy ya tare ƙwallon.
Daga baya ne kuma Pape Gueye ya ci ƙwallon da ta bai wa Senegal nasara a lokacin ƙarin lokaci, kafin hukuncin CAF ya soke sakamakon.
Hukuncin na CAF na ɗaya daga cikin matakan ladabtarwa da ke haifar da muhawara, musamman duba da yadda wasan ƙarshe ya kasance mai cike da rikice-rikice.
