Author: Abbas Ibrahim

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da tsarin gwajin shan ƙwayoyi na dole a matsayin sharadi ga duk wanda ke neman aiki a tarayya. Masu ruwa datsaki da dama sun bayyana matakin, abun da ya dace domin yaki da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya. Wannan tsari, wanda ya shafi masu neman aiki, na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na karfafa gaskiya, tsaro da kwarewa a cikin hukumomin gwamnati tare da rage barazanar da shan miyagun kwayoyi ke haifarwa. Da take martani kan wannan batu, shugabar Kungiyar dake yaki da Shan Miyagun kwayoyi wato , League Of Societal Protection Against…

Read More

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (rtd), ya jaddada cewa sabon tsarin gwajin miyagun ƙwayoyi da aka kaddamar a makarantu an tsara shi ne domin rage yawaitar shan kwayoyi a tsakanin matasan Najeriya, musamman daliban da ke neman shiga manyan makarantun gaba da sakandare. Ya bayyana cewa tsarin, wanda ya ƙunshi gwaje gwaje na dole da na bazata, mataki ne na kariya ba na hukunci ba, domin hana matasa tsunduma cikin shan miyagun kwayoyi. Marwa ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi Zababben Shugaban Jami’ar Taraba dake (TSU), Jalingo,…

Read More

Kungiyar tabbatar da da,a da daidaito akan al’amuran kudade da cigaban Al umma wato Fiscal Discipline and Development Advocacy (FIDAC) ta yi kira ga kungiyoyin fararen hula (CSOs) da su bayar da muhimmiyar gidunmowa wajen tabbatar da aiwatar da Dokokin Sauye-sauyen Haraji na shekarar 2025 tana mai jaddada cewa nasara ba kawai a wayar da kai take ba akwai bukatar shigo da Al umma A cikin wata sanarwa da shugaban ta, Abdussalam Muhammad Kani, ya fitar ya bayyana sauye-sauyen harajin a matsayin wani mataki na zamanantarwa tare da inganta tsarin haraji na Najeriya,da kuma fadada hanyoyin samar da kudin…

Read More

Mata ashirin da biyar (25) da suka Samu Lafiya daga cutsr yoyon fitsari a Gusau, Jihar Zamfara, sun kammala wani shirin koyon sana’o’i da Gidauniyar Bashir Foundation for Fistula and Women’s Health Rehabilitation ta shirya, domin dawo da mutuncinsu da kuma ƙarfafa su su dogara da kansu. Jagorar shirin, Nafisa Balarabe Abdullahi, ta bayyana cewa an horas da waɗanda suka ci gajiyar shirin a harkokin yin man shafawa (pomade) da kuma yin kayan ado na beads, sannan aka ba su kayan farawa domin su samu damar fara ƙananan sana’o’i. Ta ce shirin, wanda Asusun Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yawan Jama’a…

Read More

Rundunar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa dake Kano (NDLEA) ta sake jaddada aniyarta ta kara kaimi wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar. Kwamandan Rundunar , CN DY Lawal, ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar shugabar kungiyar Kare Al’umma Daga Shan Miyagun kwayoyi (LESPADA), Ambasada Maryam Hassan, a ziyarar ban girma data kaiwa kwamandan. Ya bayyana manyan nasarorin da hukumar ta samu wajen yakar shan miyagun ƙwayoyi, ya jaddada cewa yaki da miyagun kwayoyi alhakin kowa da kowa ne, kuma yana bukatar hadin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki. CN…

Read More

An kammala taron kwana huɗu da asusu majalisar dinkin duniya (UNFPA) ta shirya a hotel din Tahir dake garin kano, kan inganta kyawawan halayen maza, inda mahalarta suka ƙirƙiro tsare-tsare na ayyuka domin magance aurar da ƙananan yara, kaciya ga mata (FGM), da kuma cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV). Mahalarta taron, waɗanda suka fito daga kungiyoyin matasa da na al’umma daban-daban, ana sa ran za su fara aiwatar da ayyukan da aka tsara kafin 31 ga watan Disambar shekarar ta 2025. Da take jawabi a Yayin rufe taron, jami’ar UNFPA Hajiya Bahijja Bello Garko ta tabbatar da kudirin…

Read More

Kimanin Mata da kuma Yara Mata Miliyan 68 a ƙasarnan ne suka fuskanci cin zarafi ta hanyar yi musu Kachiya wanda yake nuni da cewa kimanin kaso 22 cikin Ɗari na Mata Miliyan 230 da aka yiwa Shayi a Duniya sun fito ne daga Najeriya kamar yadda aka bayyana a wani taron Bitar wayar da kai kan illlar yiwa Mata Kachiya da aka gudanar a nan birnin Kano. A yayin da take magana a rana 3 ta taron Bitar wanda yake gudana a Otel din Tahir, wata Mai rajin kare haƙƙin Mata mai suna Hajiya Karima Bungudu ta bayyana cewa…

Read More

Yau Talata ta kasance kwanaki takwas , da rasuwar mamallakin shagunan siyar da maganguna na Lamco Alhaji Ado Aminu Mai Sh inkafa wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, Daya daga cikin manajojinsa, Malam Abdullahi Idris ya bayyana dalilin da yasa aka cigaba da siyar da magunguna a shagunan duk da rasuwar mai shagunan. Da yake Jawabi a masallacin da Alhaji Ado Lamco ya gina, bayan rasuwarsa, Malam Abudullahi Idris yace tun lokacin marigayin yana raye ya bayar da wasiyya cewa ko bayan ya rasu a cigaba da siyarwa al’umma magunguna a shagunan. Yace marigayin ya jaddada cewa ko…

Read More

Daga Mustapha Muhammad Yawaitar Al’ummar Jihar Kano dake Arewa maso Yammacin Najeriya cikin hanzari, ta kasance wani babban abin damuwa, musamman a ƙoƙarin samar da isasshen abinci da aikin yi da tallafawa matasa da mata. Hakan ce ta sa karfafa wa manoma gwiwa domin noma ƙarin hatsi da nau’in tsirrai masu yaɗo, har ma da fito da hanyoyin daga darajar amfanin gona yake da matukar muhimmanci. Saboda haka ne Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tsaya kai da fata wajen sauya fasalin harkar noma a fannoni uku: haɓaka samar da amfanin gona, sarrafawa da kuma kasuwanci. A…

Read More

Shahararren Wanzami, Alhaji Musa Kawu Wanzami, ya bayyana rasuwar ɗan kasuwar Kano, Alhaji Ado Aminu (Mai Shinkafa), wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, a matsayin babban rashi da ya bar gibi mai wahalar cikewa. Alhaji Musa Wanzami, wanda ke gudanar da harkokinsa kusa da Lamco Pharmacy da ke kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 yana tare da marigayin. Ya bayyana Alhaji Ado a matsayin mutum mai karamci, sauƙin kai da tausayi, wanda ya taɓa rayuwar mutane da dama ta hanyar ayyukan alheri. A cewarsa, Alhaji Ado Lamco…

Read More