Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya sanya hannu kan Dokar Kula da Tsoffi wadda ke ba da gata na musamman ga duk ɗan asalin jihar da ya kai shekara 60 zuwa sama. Sabuwar dokar ta tanadi Albashi na wata-wata kyauta Jinya kyauta a asibitoci Sauran alawus-alawus da tallafi har zuwa rasuwa An ce manufar dokar ita ce rage raɗaɗin rayuwa ga tsofaffi, da tabbatar da walwalarsu, da kuma basu kariya ta zamantakewa bayan ritaya ko rashin ƙarfi. Masu sharhi na ganin matakin zai iya zama abin koyi ga sauran jihohi idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, tare…
Author: Abbas Ibrahim
Wani mummunan lamari ya faru a garin Keffi, Jihar Nasarawa, inda jama’a suka kashe tare da ƙone gawar wani tsohon dogari a Fadar Sarkin Keffi, da ake zargi da ƙwaƙule idanun wani yaro. An gano gawar yaron ne a cikin rami a wani gida a makwabtansu, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma. ’Yan banga sun kama wanda ake zargin, amma jama’a suka mamaye su suka yi masa duka har lahira, suka kuma banka wa gawarsa wuta. ’Yan sanda sun isa wurin, amma ƙoƙarinsu na shawo kan jama’a ya gamu da turjiya, inda wasu jami’an suka…
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gana da shugabannin manyan kasuwannin jihar, domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen rage tsadar kayan masarufi a yayin watan azumin Ramadan. Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Kwamared Sa’idu Yahaya, inda aka haɗa shugabannin kasuwannin Singer, Sabon Gari, Na’ibawa ’Yan Lemo, Dawanau, da Kasuwar Turawa ta ’Yan Kaba. Da yake jawabi a wajen taron, Kwamared Sa’idu Yahaya ya ce an kira ganawar ne domin samun fahimta da haɗin kai da ’yan kasuwa, ta yadda za a sauƙaƙa wa jama’a samun kayan abinci…
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr Abdullahi Muhammad Getso, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu tarbiyya da nagarta da su fito su shiga harkokin siyasa, domin gyara shugabanci a ƙasar. Dr Getso ya yi wannan kira ne yayin hudubar Juma’a a Masallacin Jami’ur Rahman Jumaat da ke Kundila, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane nagari da masu cancanta ke gujewa shiga takara, lamarin da ke barin siyasa a hannun masu son zuciya da rashin kishin kasa. “Hakkin al’umma ne su gano shugabanni nagari, su ƙarfafa musu gwiwa su nemi shugabanci, domin al’umma ta amfana da adalcinsu da…
Shugaban Kwango Brazzaville, Denis Sassou Nguesso na kasancewa shugaba a nahiyar Afirka da ya fi dade wa kan karagar mulki bayan takwarorinsa na Kamaru, Paul Biya da kuma Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Eauatorial Guinea. Shugaban ƙasar Congo-Brazzaville, Denis Sassou Nguesso, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga Maris, 2026, domin ƙara tsawaita mulkinsa da ya shafe sama da shekaru 40 yana yi. Sassou Nguesso mai shekaru 82, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi gaban dubban magoya bayansa a…
Wasu ‘yan daba sun kai hari hedikwatar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta Jihar Edo a daren Laraba, inda suka lalata kadarorin jam’iyyar tare da yin yunkurin ƙona ginin. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fasa tagogi tare da lalata wasu kayayyaki a hedikwatar jam’iyyar da ke kan titin Ogbelaka a Birnin Benin. Sai dai, mazauna yankin da magoya bayan jam’iyyar sun dakile yunkurin kafin lamarin ya kazance. PREMIUM TIMES ta rawaito cewa a wani bidiyo da ke yawo a shafin Facebook, wani mutum da ake zargin mamba ne na ADC ya bayyana yadda harin ya faru, inda ya nuna…
Jam’iyyar African Democratic Party (ADC) ta soki dokar gyaran haraji ta Gwamnatin Tarayya, inda ta bayyana ta a matsayin wadda ke cutar da al’umma tare da barazanar jefa kasar cikin karin matsin tattalin arziki da rashin daidaiton zamantakewa. Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a sassan kasar, inda ta bayyana cewa halin da ake ciki a matsayin abin tausayi da ke kara haifar da rashin aminci tsakanin jama’a da gwamnati, sakamakon kasa cika alkawuran da aka sha yi na kare rayuka da dukiyoyi. Wadannan batutuwa na kunshe ne a cikin sakon Kirsimeti da jam’iyyar…
Shugabar Hukumar Kula da Tsarin Kiwon Lafiya na taimakekekiya ta Jihar Kano (KSCHMA), Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta yi kira da a karfafa hadin gwiwa da shugabannin mata a kungiyoyin kwadago domin fadada wayar da kai da kuma amfanin shirin inshorar lafiya na jihar. Dakta Rahila Mukhtar ta bayyana hakan ne yayin da ta halarci Taron Tsare-tsaren Dabaru na Shugabannin Kwamitin Mata na Ƙungiyoyin Kwadago yayinda taron ke gudana . Duk da cewa ta isa taron ne a tsakiyar shirin, ta gabatar da cikakken bayani kan Tsarin Inshorar Kiwon Lafiya na Jihar Kano, inda ta yi bayani kan ayyukansa,…
Alhaji Aminu Baba Dan,agundi yace Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bashi da wani Hurumi na bada Shawarar Janye Jami’an tsaron Gidan Sarki na Nassarawa Yace “Maganar da take kotu to Kai waye zakayi wannan maganar a Matsayin kana wa?” Sanarwa da Abubakar Balarabe Kofar Na, Isa ya bayar ta ruwaito Amina Babba na cewa “Baka da wani Hurumi akan wannan, kuma koshi Gwamnan Kano Bashi da wannan Hurumin.” Sarkin Dawaki Babba ya kara da cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kotu ce ta bashi wannan tsaro ba Gwamnati ba. A don haka ne ma yace wannan maganar da Sanata Rabiu…
´ Taron jama’a mai yawa ne , safiyar ranar Talata yayi Tururuwa domin halartar jana’izar Muhammad Sani Hassan, wanda aka fi sani da Sanin Kale, a unguwar Yakasai da ke cikin ƙaramar hukumar Municipal. Sanin Kale, wanda bai yi wata rashin lafiya ba, ya rasu ne bayan ya kammala sallar Isha’i. Ƙanwarsa, Zainab Hassan wadda aka fi sani da Ta’annabi, ta bayyana cewa Sani, wanda ya shahara a unguwar, ya yi wasa da yara tare da raba musu alewa kaɗan kafin rasuwarsa. Wani mazaunin yankin, Mohammed Yakasai, ya ce: “A nan kusa bamu ga irin wannan taron jama’a mai yawa…