Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu
Daga Abdullahi Yusuf
Allah Mai yi da a yi,wai yanzu a kasata ta gado, Nigeria,an wayi gari man fetur ya wadata,har ma ya yi yawa,kamar ya biyo masu ababan hawa har gidajensu.
Wai a yau,man fetur din da a da a ke nema kamar Ruwan Bagaja, sai ga shi yanzu a na neman kai da shi,masu gidajen mai su na kira,wani zubinma har da rokon masu ababan hawa,domin su zo su saya.
Idan kuma an saya din,sai ka ga masu sayarda fetur din su na ta fara’a da godiya,kamar ba su ne ba a da su ka rika yin yanga su na gallazawa masu motoci da babura wajen sayar musu da man fetur din.
An dai sani cewa man fetur din ya wadata ne bayan da Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ta janye tallafin man fetur, wanda daga nan ne a ka shiga ruguntsumin hada-hadarsa, lokacin da kuma masu gidajen man fetur din su ka boye man fetur din da ke cikin tankunansu,wanda su ka saya da tallafin Gwamnati a ciki.
Daga nan sai wadannan Bayin Allah su ka rika fito da tsohon man fetur din da su ka saya a kan farashin N230 ko sama da haka, a kan lita daya, a lokacin tallafi, da kadan-kadan,su na sayar da shi N900 a kan lita daya,har sai da man ya kai N1,500 lita daya,kuma ma babu shi a gidajen man.
Wannan halin ya sanya tilas masu ababan hawa da yawa su ka hakura da man fetur din.Wadansu daga cikinsu ma suka sayarda motocinsu,wadansu su kuma su ka koma amfani da babura domin samin sauki.
Da sannu,sai farashin man ya rika saukowa, har ya kai a na sai da shi kasa da N1000 a yanzu,sai dai matsalar ita ce yawancin mutane ba sa iya sayensa da yawa saboda halin matsin tattalin arzikin da a ke ciki.
Sai ka ga mutum ya zo gidan mai da babbar mota ya ce a zuba masa na N5000,abin takaici, abin tausayi.Wannan halin ne ya sanya man fetur din ya taru tinjim a gidajen man,a na so a saya,amma ba bu kudin sayen.
Saboda haka yanzu a Nigeria, man fetur ya fi saukin samu a saya,fiye da ruwan sha, musamman ma a wasu garuruwan da masu karamin karfi ke zaune.
Za ka ga mai sayar da ruwa a cikin kura a na kiransa ya na yanga, ya na wulakanta masu saya,har ya na fada musu bakaken maganganu,amma a waje daya masu sayarda man fetur su na roko a zo a saya.
Wannan yanayi ba wani ci gaba ba ne,kawai nuni ne ga yadda kasuwar man fetur ta kasance a halinzu, wato,”Ga Koshi Ga Kwanan Yunwa.” Allah Shi kyauta.