Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gana da shugabannin manyan kasuwannin jihar, domin tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen rage tsadar kayan masarufi a yayin watan azumin Ramadan.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Kwamared Sa’idu Yahaya, inda aka haɗa shugabannin kasuwannin Singer, Sabon Gari, Na’ibawa ’Yan Lemo, Dawanau, da Kasuwar Turawa ta ’Yan Kaba.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamared Sa’idu Yahaya ya ce an kira ganawar ne domin samun fahimta da haɗin kai da ’yan kasuwa, ta yadda za a sauƙaƙa wa jama’a samun kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki a lokacin azumi.
Ya jaddada cewa hukumar na fatan ’yan kasuwa za su yi la’akari da halin da al’umma ke ciki, tare da kauce wa tashin farashi a wannan lokaci mai muhimmanci ga Musulmi.
A nasa ɓangaren, Shugaban Kasuwar Singer kuma Shugaban Shugabannin Kasuwannin Kano, Barista Junaidu Muhammad Zakari, ya ce ’yan kasuwa a shirye suke su ba da gudunmawa domin rage farashin kayayyakin yau da kullum, musamman a watan Ramadan.
Haka kuma, shugaban hukumar ya jajanta wa ’yan kasuwar Singer bisa gobarar da ta auku a kasuwar, inda ya yi addu’ar Allah Ya maye musu asarar da abin da ya fi alheri.
