Tsokaci Kan Alamun Tsufa
Daga Abbas Ibrahim
Kwararru masu kula da masu cutar sankara,wato cancer, a harshen turanci,sun yi tsokaci a kan irin alamun da Dan Adam ya ke nunawa idan Tsufa ya zo masa.
Alamun,in ji masanan,sun hada da canje-canjen halaye da kuma kalubalen zamantakewa wadanda da ke tattare da yanayin Tsufa.
Suka ce,shi Tsufa ya na fara zuwa ne daga lokacin da mutum ya cika shekaru 60 da haihuwa,daga nan zai yi ta tsufa har ya kai zuwa shekaru 80,90 har inda Allah Ya so.
Daga nan sai masanan su ka ce Kadaici ya na daga cikin matsalolin da ke addabar tsofaffi maza,saboda yawancinsu ba safai su ke tsufa ta re da mataikunsu ba,ga shi kuma a na ganin sun zame wa na kusa da su wani babban nauyi.
Saboda haka, masanan sun shawarci tsofaffi da su rika yin mu’amala da mutane,su kuma rike mutuncinsu,tare da cin irin abincin da za ya taimaki lafiyarsu.
Suka ce,kamar yadda shahararren marubucin Adabin Turancin nan,wato William Shakespeare ya ce,”yawancin matsalolin rayuwa masu wucewa ne,kuma a na iya maganinsu,amma ban da mutuwa.
Saboda haka, kwararrun sun shawarci masu yawan shekaru da su kasance masu hakuri,nuna halin dattako da kuma rayuwa mai ma’ana, sannan kuma su yarda da ikon Allah.
